✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tafiyar Hawainiya da Buhari ke yi ta yi yawa —Baba-Ahmed

"Ba za mu iya jiran ka har lokacin da kake tunanin yin gyara ba".

Mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Hakeem Baba-Ahmed, ya ce tafiyar hawainiyar da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi a yanayin jagorancinsa ta yi yawa.

Baba-Ahmed ya yi wannan furuci ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Arise a ranar Laraba.

Da yake amsa tambaya kan irin shawarar da zai bai wa Shugaba Buhari, Baba-Ahmed ya ce ba ta wuce Shugaban ya tashi tsaye wajen gudanar da aiki domin magance rushewar kasar ba.

“Da zan samu damar zantawa da shi, zan fada masa cewa ya ta shi tsaye saboda kasar nan na kan gabar wargajewa.

“Ana cikin tsaka mai wuya, komai sai kara tabarbarewa yake yi a gwamnatinka.

“An rantsar da kai a 2015, aka sake rantsar da kai a 2019 kuma ka yi alkawarin kare rayukan al’umma.

“Sai dai a yanzu Shugaban Kasa ka gaza sauke nauyin da rataya a wuyanka, amma ina da yakinin cewa za a samu mafita matukar wannan gwamnati ta yi amfani da shawarwarin da ake ba ta.”

Dattijon ya ci gaba da cewa, “Abu na biyu, yana da kyau ka ja gwamnoni a jika, domin su yi ayyukansu yadda ya kamata saboda akwai nauyin da ya kamata su sauke kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada; Musamman abin da ya shafi matsalar tsaro. Me kuke ganin ya dace? Me za mu iya yi tare? Me zan iya muku don warware matsalolin da suka dame ku?” inji Baba-Ahmed.

“Abu na uku, idan aka yi duba na tsanaki game da matsalar tsaro a kasar nan, za a ga cewa akwai wani abu da yake tafiya ba daidai ba don kodayaushe sauye-sauye kake yi amma hakan ba ya wani tasiri.

“Ko dai yanayin mu’amalarka a matsayinka na Babban Kwamandan Tsaron Kasa ba daidai kake yi ba, ko kuma wanda ka aminta da su wajen ba mu kariya ba daidai suke aikatawa ba.

“Mai yasa aka kasa ba mu tsaro? Shin me ya sa Najeriya ta kasa maganin ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane? Shekaru uku da suka wuce ba a wadannan abubuwan.”

“Da akwai wanda yake tambayar kansa me ya sa irin wadannan abubuwa ke faruwa a kasar nan? Shin kana da kyakkyawar fahimta a tsakaninka da hukumomin tsaron kasar nan kuwa?

“Kana da hanyoyin magance matsalolin da suka addabe mu? Saboda ba za mu iya ci gaba da zaman jira har zuwa lokacin da za ka gyara kasar nan ba.

“Tafiyar hawainiyarka da kake yi ta yi yawa, shi ya sa mutane da dama suka gaji, suke ganin ba za su ci gaba da kasancewa ’yan Najeriya ba,” a cewarsa.