✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ababen hawa na lalacewa bayan NNPC ta shigo da gurbataccen mai lita 100m

An kiyasta cewa kudin gurbataccen man da NNPC ta shigo da shi ya kai Naira biliyan 16.5

Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya tabbatar da cewa yana kokarin janye gurbataccen man fetur na kimanin Naira biliyan 16.5 da ya shigo da shi Najeriya.

Majiyoyi masu tushe sun tabbatar wa Aminiya cewa NNPC ta shigo da lita miliyan 100 na gurbataccen fetur mai dauke da sunadarin methanol fiye da kima —duk da cewa NNPC bai bayyana adadin man da ya shigo da shi ba.

Sanawar da Hukumar Mai na Kan Tudu (NMDPRA), wadda ke karkashin NNPC, ta tabbatar cewa, “Mun gano wani adadi na man fetur mai dauke da sunadarin methanol fiye da adadin da Najeriya ta kayyade da ke yawo a kasuwanni,” ta kuma bayyana kokarin da NNPC ke yi na janye shi daga kasuwa.

Tuni dai masu ababen hawa suka fara shiga damuwa ganin yadda aka samun labarin cewa ababen hawan wadansu da suka riga suka sha gurbataccen man suna ta lalacewa.

A hirar da aka yi da shi a Sashen Hausa na BBC, Shugaban NMDPRA, Faruq Ahmed, ya ce, “Jiragen ruwa hudu na dakon man fetur ne aka shigo da su Najeriya, wadanda muka gano man da suke saukewa na dauke da sunadarin methanol fiye da kima.”

Ta ce, “Amma domin tabbatar da lafiyar ababen hawa da injina, an kebe shi wannan gurbataccen man da wuraren da ya shiga domin janye shi daga kasuwa da kuma motocin da suka fara dakon shi.”

NMDPRA ta bayyana cewa methanol sunadari ne da a koyaushe ake amfani da da shi wajen tace man fetur, kuma “An gano kamfanin da man ya shigo ta wurinsa, kuma NNPC da NMDPRA za su dauki matakan da suka dace na kasuwanci da sauransu da suka dace.”

Aminiya ta kuma gano cewa wani kamfani daga kasashen Turai ne ya shigo da gurbataccen man Najeriya a madadin NNPC.

Kawo yanzu dai hukumar NNPC, wadda ita kadai ke shigo da tataccen mai Najeriya ba ta bayyana me ya faru har kamfanin ya shigo da gurbataccen man ba.

Janye gurbataccen man daga kasuwa

Faruq ya ce, bayan gano gurbataccen man, hukumarsa ta, “Dakatar da daukacin jiragen daga ci gaba da sauke man, muka kuma hana dafo-dafo da aka sauke man a Warri da Kalaba fitar da shi.

“Mun kuma yi nasarar dakatar da yawancin motocin da suka yi dakon wannan man, sai dai kuma wasunsu sun riga sun sauke a gidajen mai; Amma duk da haka, mun yi nasarar jenye man daga gidajen man.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa hukumar tare da saurana masu ruwa da tsaki a bangaren man fetur na yin wani zama a Legas kan hanyoyin da za a tabbatar da samuwar wadataccen mai a fadin Najeriya.

Faruq Ahmed ya kara da cewa, “A yanzu haka mun kafa wani kwamiti mai wakilai daga NNPC, NMDPRA, manyan dillalan mai da dillalai masu zaman kansu, suna tattaunawa a Legas kan yadda za a janye gurbataccen man daga kasar nan, sannan a samar da mai kyan kasuwanni.”

“Mun kuma gano kamfanin da ya shigo da man, ya sayar wa NNPC, kuma za mu dauki matakin shari’a a kan kamfanin. Abin da ya shafi kasuwanci kuma NNPC za da dauka.”

Babbar asara

’Yan kasuwa da masu lura da harkokin man fetur sun kiyasta cewa kudin gurbataccen man ya kai Naira biliyan 16.5.

Sun kuma bayyana cewa kawo yanzu wasu ababen hawa da suka yi amfani da gurbataccen man sun lalace.

Wakilinmu ya ruwaito cewa saboda gazawar NNPC wajen tace danyen mai, Najeriya kan fitar da danyen zuwa kasashen waje sannan ta shigo da tataccen domin amfani a cikin gida.

Wasu dillalan mai sun shaida wa Aminiya cewa tuni gurbataccen man ya fara yawo a wasu gidajen mai a Legal da Abuja da kuma jihohin Delta da Kuros Riba.

Daga Sagir Kano Saleh, Simon E. Sunday, Chris Agabi, Hamisu K. Matazu (Abuja), Abdullateef Aliyu & Eugene Agha (Legas)