✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adalci da gaskiya ne mafita daga rashin tsaro a kasar nan – Sanata Kabiru Marafa

Sanata Kabiru Garba Marafa shi ke wakiltar Zamfara ta Tsakiya a Majalisar Dattawa a zantawa da Aminiya ya ce mafita daga rashin zaman lafiya ita…

Sanata Kabiru Garba Marafa shi ke wakiltar Zamfara ta Tsakiya a Majalisar Dattawa a zantawa da Aminiya ya ce mafita daga rashin zaman lafiya ita ce yin adalci da gaskiya. Kuma ya nuna damuwa kan kalaman batanci ga ’yan Arewa da ya ce sun fito daga shugaban kwamitin taron kasa, Sanata Femi Okoronmu, inda ya nemi Shugaban Jonathan ya tsige shi:

Sanata Kabiru MarafaAminiya: Mene ne ra’ayinka game da taron kasa da ake shirin yi nan gaba?
Sanata Marafa: A matsayina na dan Adam kuma a madadin yankin da nake wakilta kuma dan Arewa, ba na jin akwai wani taro da za a yi a kasar nan da zai tsorata ni. Na yarda da Najeriya a matsayin kasa daya amma ba zan taba yarda wani ko wasu su fada min yadda zan rika gudanar da rayuwata ba. Ba zan yarda wani ko wasu su rika fada min irin kayan da zan rika sanyawa ko addinin da zan yi ba. Idan har za mu ci gaba da kasancewa ’yan kasa daya dole mu rika mutunta juna. Dole ne ka girmama ni da al’aduna da addinina da kuma girmama duk wani abu da nake mutuntawa ta haka ne za mu iya zama domin ni ma in saka maka.
Aminiya: Wasu na tsoron idan aka yi taron kasa akwai yiwuwar kasar nan ta rabu, wasu na alakanta taron da shirin Shugaban Jonathan na neman tazarce, mene ne ra’ayinka?
Sanata Marafa: Gaskiya idan aka yi la’akari da shugaban kwamitin babu yadda za a yi a ce babu wata makarkashiya game da shi. Misali shugaban kwamitin a wata hira da jaridar Leadership ta ran 16 ga Nuwamba, 2013 ya ce sai da ya yi shekara 30 yana kiran a gudanar da taron kasa. Idan har za a ce mutum na bin abu daya a tsawon wadannan shekaru dole ne a ce akwai wani abu ko manufa da yake neman ya cimma. Mutumin nan shi ne a wata hira da ya yi da jaridar National Mirror ta ran 12 ga Fabrairun bana, ya kwatanta Shugaban Jonathan da wasu kalamai marasa dadi amma duk da haka aka dauko shi aka ba shi shugabancin wannan kwamiti. Saboda haka duk yadda ka kai da kauce wa tunanin cewa kila akwai makarkashiya da ta sanya ake son shirya wannan taro ba ka iya kaucewa. Amma abin da kawai sauran mutane suka dauka shi ne ’yan Arewa na adawa da taron. Ni kuma ina dada fada musu cewa kila masu jin tsoron ’yan Arewa na da ne. Amma yanzu akwai ’yan Arewa da yawa da ba su jin tsoron wannan taro. Wasu na daukar ’yan Arewa a matsayin ’yan tsaki ne, kawai da an watsa musu hatsi ko tsaba shi ke nan, duk wannan shirme ne. Mun dade muna zaune a matsayin kasa daya kafin wata kasa mai suna Najeriya ta bullo. Ka duba lokacin Jihadin Usman danfodiyo wanda aka yi a shekarar 1804. Kuma a lokacin muna zaune ne cikin farin ciki da juna tun babu Najeriya ballantana wani abu wai shi man fetur. An kirkiro Najeriya ne a 1904 shekara 100 bayan danfodiyo kuma aka ba ta ’yanci a 1960 idan ka duba shekaru nawa ke nan daga shekarar 1804 zuwa 1960. Wane amfani muka samu daga man fetur, ta wace hanya fetur ya amfani mutane? Saboda haka ina ganin akwai wata makarkashiya da suke kokarin boyewa. Akwai Majalisar Dokoki ta kasa kuma duk manufa da aikin wannan kwamiti abubuwa ne da suka shafi kundin tsarin mulkin kasa da ke cikin hurumin majalisa. Suna kuma sane cewa taron zai lashe makudan kudi da daukar lokaci wajen tattaunawa. Bayan suna sane cewa akwai wadanda alhakin haka ya rataya a wuyansu. Saboda haka ina ganin ’yan Najeriya sun yi daidai da suke nuna shakku a kan dalilin da ya sa ake son shirya taron. Sannan ga shi shugaban kwamitin shirya taron mutum ne da ke kiyayya ga Shugaban kasa idan ka dubi hirar da ya yi da jaridar National Mirror ta 12 ga Fabrairu, 2013.
A cikin hirar ce ya ce wai idan makiyinka ya ba ka wani abu da ka san zai amfani kasarka ya dace ka karba. Ka ga a nan ke nan yana kwatanta Shugaban kasa a matsayin makiyinsa ke nan.  Kuma sai ga shi Shugaban kasa ya ba shi damar da ya ce ya dauki shekara 30 yana nema. Ka ga ke nan ya amsa ne domin ya cimma burinsa a yanzu. Baya ga wannan, mutumin nan matsoraci ne domin a hirarsa da jaridar Leadership ya ce wai an shirya yin taron ne saboda akwai wadanda ke adawa da taron. Amma ya ki ya ambaci ko su wane ne, saboda wai ’yan Najeriya suna sane da dalilan da ya sa suke adawa da taron.Ya kamata ya taimaka wajen rage asarar kudin jama’a da za a a yi sanadiyyar shirya taron wajen bayyana mutanen da suke nuna adawarsu ga taron.  
Aminiya: Ina mafita daga rashin tsaro da kasar nan ke fama da shi?
Sanata Marafa: Adalci da gaskiya ne mafita daga rashin tsaro a kasar nan. Duk zancen da ake yi a kan rashin tsaro a Najeriya rashin adalci ke kawo shi. Idan muka kawar da da rashin adalci da son kai zai yi matukar taimakawa wajen kawar da wannan al’amari. Saboda in mutum ya ji a ransa ba a yi masa adalci zai ji ba dadi.  Kamar yadda nake fadi ina matukar son kasancewar Nejeriya kasa daya, amma ba fa ba zan yarda wani ko wasu su rika yi min shishigi ta hanyar neman nuna min irin shigar da zan yi ba, saboda dukkanmu ’yan Najeriya ne kuma hakkinmu ne mu kare ta. Najeriya kasa ce da ke da kabilu daban-daban da kuma addinai. Saboda haka idan har za mu zauna tare a matsayin kasa daya al’umma daya, dole ne mu rika mutunta junanmu. Kamata ya yi a ce babu wanda ya fi karfin doka wannan shi zai magance rashin tsaro.
Aminiya: Kana ganin shugabannin Najeriya za su iya yin adalci da gaskiya kuwa?
Sanata Marafa: Me zai hana, ai ba su da bambanci da sauran shugabannin kasashen duniya. Abin da kawai suke bukata shi ne jajircewa a kan haka.