✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin Hajji da Darare Goma

Masallacin Annabi, Madina Fassarar Salihu Makera Hamdala da salati. Bayan haka ku bi Allah da takawa ya ku Musulmi! Saboda takawa ita ce mafi alherin…

Masallacin Annabi, Madina

Fassarar Salihu Makera

Hamdala da salati.

Bayan haka ku bi Allah da takawa ya ku Musulmi! Saboda takawa ita ce mafi alherin guzuri domin Ranar Hisabi da ita Allah Yake kyautata al’amuran bayi. “Duk wanda ya bi Allah da takawa, (Allah), Zai sanya masa sauki a cikin al’amuransa.” (Dalak:4).

Ku sani ya bayin Allah! Lallai ibada hakki ne na Ubangijin talikai a kan mukallafai, kuma farilla ce da aka yi wa hatimi a kan mutane da aljanu. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ban halicci aljanu da mutane ba face domin su bauta Min.” (Zariyati:56).

Ibada ita ce mafi daukakar abin da Allah Ya karrama bayinSa da ita. Kuma da ita Yake daukaka masu takawa. Da ibada zukata suke yin haske da ibada zukata suke tarbiyyantuwa, dabi’u su daidaita, hankula su kyautata, ayyuka su tsarkaka, rayuwa ta inganta ta kyautata iyakar kyautatawa. Sai kuma Allah Madaukaki Ya yarda da bawa, kuma a samu daukaka a cikin Aljanna, a kankare zunubai a ninninka kyawawan ayyuka.

Daga cikin rahamar Allah gare mu, akwai aiko mana da mafi alherin halitta Annabi Muhammad (SAW), yana mai bayyana mana abin da Ubangijinmu Ya yarda da shi gare mu na daga maganganu da ayyuka da kudurce-kudurce, yana yi mana gargadi daga abin da zai fusata Ubangijinmu na maganganu da ayyuka da kudurce-kudurce. Allah Madaukaki Ya ce: “Kamar yadda Muka aiko a cikinku wani Manzo daga cikinku, yana karanta ayoyyinMu a kanku. kuma yana sanar da ku Littafi da Hikima kuma yana sanar da ku abin da kuka kasance ba ku sani ba. Kuma ku tuna Ni, Ni kuma in tuna ku, ku gode Min kada ku butulce Min.” (Bakara: 151-152).

Ba domin Allah Ya aiko da Manzanni (AS) kuma Ya saukar da Littattfai tare da su ba, da dan Adam ya fi dabba bacewa, amma sai Allah Ya yi rahama ga mutane, Ya shar’anta addini Ya yi komai daki-daki, Ya daidaita alamun shiriya, masu rabo suka shiryu, shakiyyai suka kauce wa bayananSa.

Daga cikin rahamar Allah da hikimarSa da cikar iliminSa, sai Ya shar’anta ibada domin gyara zuciyar dan Adam, Ya shar’anta ibadoji iri-iri; Sallah da Zakka da Azumi da Hajji da sauransu, domin tabbatar da cikar tarbiyyar mutum da tsarkake shi ta kowace fuska. Allah Madaukaki Ya ce: “Allah ba Ya nufin Ya sanya wani kunci a gare ku, sai dai Yana nufin Ya tsarkake ku ne kuma Ya cika ni’imarSa a kanku, tsammaninku kuna godewa.” (Ma’ida: 6).

Hajji rukuni ne daga cikin rukunan Musulunci, kuma Allah Ya tara dukan ayyukan ibada ta zuciya da ikhlasi a cikinsa, kuma Ya tara ibada ta dukiya da magana da ta gabbai a cikinsa. Zamanin Hajji ya kunshi kalmar shahada, wadda ita ce mafi girman rukunan Musulunci. Ya tara Sallah da ciyar da dukiya da azumi ga wanda bai samu hadaya ba da umarni da alheri da hana munkari da hakuri da hadiye fushi da tausayawa da jinkai da sanin alheri da yakar zuciya daga sabo da sauran ayyukan da Allah Ya farlanta. Kuma ya kunshi guje wa haramtattun ayyuka. Hajji aya ce daga cikin ayoyin Allah masu girma da ke nuna cewa abin da Annabi Muhammad (SAW) ya zo da shi, shi ne addinin gaskiya. Babu wata hukuma ko gwamnati ko wani karfi a duniya da zai iya tara mahajjata kowace shekara daga sassan duniya daga dukan nau’o’in mutane masu mabambantan matsayi da jinsi su zo da zuciya cike da shauki da soyayya suna masu mance wahalar doguwar tafiyar da suka sha, suna masu farin ciki da barin kasashe da iyalai da abokansu, suna ji a jikinsu cewa lokacin aikin Hajji, shi ne lokaci mafi sa’ada a rayuwa, suna girmama ayyukan Hajji suna ciyar da dukiya domin Hajji cikin jin dadi. Babu mai iya haka sai Allah Wanda sunanSa ya daukaka, siffofinSa suka girmama. Shi ne Ya ce da BadadayinSa Ibrahim (AS): “Ka yi kira a cikin mutane su zo maka a kafafu da duk wani mai daukar kaya, su zo daga kowane lungu mai nisa. Domin su halarci wasu abubuwan amfani gare su, kuma su ambaci Allah a wasu ranaku sanannu kan abin da aka azurta su na daga dabbobin ni’ima. Ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da mayunwanci, fakiri.” (Hajji: 27-28).

Ibn Jarir da Ibn Kasir da wadansu masu tafsiri sun cirato daga Ibn Abbas (RA) cewa, lokacin da Allah Ya umarci Annabi Ibrahim (AS) ya yi kira ga mutane su zo aikin Hajji ya ce: “Ya Ubangiji! Yaya zan isa ga mutane alhali sautina ba zai je gare su ba? Sai (Allah) Ya ce: “Ka yi kira isarwa tana kanMu. Sai ya tashi tsaye a inda yake. Wadansu suka ce a kan Dutse Marwa wadansu suka ce a Dutsen Safa, wadansu suka ce a Abu Kubais. Ya ce: “Ya ku mutane! Lallai Ubangijinku Ya riki gida ku yi hajjinsa. Sai aka ce: “Lallai duwatsu sun sunkuya (sun dauki) sautin ya isa dukan sassan duniya, har ya isa ga wanda ke cikin mahaifa da tsatso. Kuma kowane abu da ya ji na daga dutse da marmara da itatuwa ya amsa masa: “Laibaikal lahumma labaika!” Allah Ya rubuta wanda zai yi Hajji har zuwa Ranar Kiyama.”

An so ga mahajjaci da wanda bai yi ba su yi gaggawar zuwa ga kowane alheri da aiki nagari da da’a a goman farko na watan Zul-Hajji. An karbo daga Ibn Abbas (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Babu wasu ranaku da aiki nagari ya fi soyuwa ga Allah kamar wadannan ranaku, (yana nufin goman farko na Zul-Hajji)” Suka ce: “Ya Manzon Allah! Koda jihadi a tafarkin Allah?” Ya ce: “Koda jihadi a tafarkin Allah, sai dai in mutum ya fita da ransa da dukiyarsa bai dawo da komai daga cikinsu ba.” Buhari ya ruwaito.

Domin haka ana son yawaita ambaton Allah a cikin masallatai da hanyoyi da wuraren taro da kasuwanni da wuraren aiki da yayin da mutum ya kebanta shi kadai.

A cikin wadannan kwanaki goma ake samun Ranar Arfa. Dan uwa Musulmi koda tsayuwar Arfa ta kubce maka, Allah Ya shar’anta maka azumtarta. An karbo daga Abu Kattada (RA) ya ce: “An tambayi Manzon Allah (SAW) game da azumin Ranar Arfa sai ya ce: “Yana kankare zunubin shekarar da ta gabata da wadda ake ciki.” Muslim ya ruwaito. Kuma an karbo daga Ibn Umar (RA) daga Annabi (SAW) lallai shi ya ce: “Babu wasu ranaku da suka fi girma a wurin Allah kuma aiki ya fi soyuwa gare Shi a cikinsu daga wadannan ranaku goma. Don haka ku yawaita tasbihi da takbiri da tahmidi a cikinsu.” Ahmad ya ruwaito. Don haka ne Ibn Umar da Abu Huraira (RA) suke fita kasuwa su rika kabbarori mutane suna koyi da su. Kamar yadda Buhari ya ruwaito.

Ku yi riko da ladubban Musulunci madaukaka da dabi’unsa kyawawa, ku yawaita tuba a cikin watan Zul-Hajji ku gyara ayyukanku ku ji tsoron abin da zai zo gaba. Ku yi nadama kan abin da ya gabata a rayuwarku. Ku gode wa Allah Madaukaki ku yi maSa shukura a bisa ni’imar zaman lafiya da imani da abubuwan da Ya hore muku na alherai da ibadoji. Ku gode maSa kan abin da Ya ba ku na arziki da biyan bukatu da abin da Ya kare muku na daga ukubobi da cututtuka.

Bayin Allah, “Lallai, Allah da mala’ikunSa suna salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.” (K:33:56).

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya yi salata a gare ni, Allah zai yi masa salati goma a madadinta.” Don haka ku yi salati a kan Shugaban Mutanen Farko da na Karshe, kuma Shugaban Manzanni. Allahumma salli ala Muhammad wa ala ali Muhammad kama sallaita ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim, innaka hamidun majid. Wa barik ala Muhammad wa ali Muhammad kama barakta ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim, innaka hamidun majid.

Ya Allah! Ka yarda da sahabban AnnabinKa baki daya da tabi’ai da tabi’ut tabi’ina da wadanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako, Ka hada da mu a cikinsu don rahamarKa ya Mafi rahamar masu rahama.

Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da Musulmi, Ka kaskantar da shirka da mushirikai, Ka darkake makiya addini, Ka ruguza taron masu sauyawa da jikirtawa daga kungiyoyin ’yan bidi’a baki daya. Ya Allah! Ka sanya wannan kasa tamu da sauran kasashen Musulmi su zauna lafiya cikin wadata da yalwa.