✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin tsaro a garin Jos na kowa ne – DPO Ibrahim

Babban Jami’in ’yan sanda (DPO) na shiyar Laranto da ke garin Jos a Jihar Filato, Alhaji Saleh Ibrahim ya ce aikin samar da tsaro a…

Babban Jami’in ’yan sanda (DPO) na shiyar Laranto da ke garin Jos a Jihar Filato, Alhaji Saleh Ibrahim ya ce aikin samar da tsaro a garin Jos da Najeriya baki daya na kowa da kowa ne.
Alhaji  Saleh Ibrahim ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro da ’yan kungiyar sintiri suka shirya a Jos, inda ya ce ya kamata  ’yan sanda da sojoji da jami’an hukumar kiyaye hadarurruka da  jami’an tsaron farin kaya da ’yan banga da  kowa a taru a hada kai a sanya ido don a ci gaba da samun  zaman lafiya a Jos da Najeriya.
Ya ce babu shakka daukar wannan mataki zai taimaka wajen magance halin da aka shiga ta matsalar tsaro a kasar nan.
DPO Ibrahim ya ce ayyukan kungiyar ’yan sintiri abin a yabawa ne, saboda sun sa an kara samun zaman lafiya a garin Jos da Jihar Filato baki daya.
Ya ce “Mu ’yan sanda idan ’yan banga suka ci gaba da gudanar da irin wadannan ayyuka, a shirye muke mu dada hannu da su don a ci gaba da samun zaman lafiya.”
Mataimakin Kwamandan kungiyar ’Yan Sintiri ta Najeriya na shiyyar Arewa ta Tsakiya Alhaji Garba Juji ya ce a shirye kungiyar take ta tallafa wa jami’an tsaron Najeriya wajen kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan.
Ya ce ’yan sintiri suna tare da al’umma ne sabanin sauran jami’an tsaro, don haka suna da rawar da za su taka wajen magance matsalar tsaro a kasar nan. Sai ya yi kira ga gwamnati da al’ummar Najeriya su taimaka wa kungiyar don ta samu nasarar aikinta.
Kwamandan kungiyar na karamar Hukumar Jos ta Arewa Alhaji Idris Sulaiman ya ce an shirya taron ne don mika wa ’yan kungiyar da suka halarci taron kara wa juna sani da kungiyar shiyyar Arewa ta Tsakiya ta shirya kwanakin baya a Minna takardun shaidar halartar taron.