✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin yi ga matasa ne kashin bayan zaman lafiya a arewa – Sarkin ‘Yan Gwangwan

A daidai lokacin da ake fuskantar matsalar rashin tsaro a wasu yankunan jihohin Arewa masu fashin baki na ci gaba da bayyana matakan da suka…

A daidai lokacin da ake fuskantar matsalar rashin tsaro a wasu yankunan jihohin Arewa masu fashin baki na ci gaba da bayyana matakan da suka kamata a dauka domin kawo karshen matsalar. Alhaji Ibrahim Abdullahi Soja Sarkin ’Yan Gwangwan na jihohim Yamma ya ce samar da aikin dogaro da kai ga matasa a Arewa shi ne kashin bayan wanzuwar zaman lafiya a yankin.

Ya ce masu hannu-da-shuni a  Kudu sun yi wa takwarorinsu na Arewa fintinkau wajen samar wa matasansu abubuwan dogaro da kai, inda suke tallafa wa ilimin al’ummarsu tare da kirkirar kanana da matsakaitan masana’antu domin amfanar al’ummarsu, “Kamata ya yi mu ma a Arewa masu hannu- da-shuninmu su fara tunanin me za su yi su rage zaman banza a tsakanin matasanmu, idan ka lura mawadatanmu na Arewa sun fi gane wa su tara jama’a a kofar gida ana zaune ana yi musu fadanci ko maula idan gari ya waye su bi jama’ar suna raba musu Naira 200 ko 500, wani ma Naira 50 za a ba shi. Ka ga wannan ba hanya ce mai dorewa ba, domin duk mutumin da zai ba ka yau gobe ya ba ka wata rana sai ya gaji da kai,’ inji shi.                                                                                                                                                Ya ce “Maimakon haka kamata ya yi mu rika tunanin kafa masana’antu da ’ya’yanmu za su samu aikin yi, ba zai yiwu mu sakar wa gwamnati komai ba, domin gwamnati ba za ta iya samar wa kowa aikin yi ba, idan masu halin cikinmu suka ba da tasu gudunmwar za a samu sa’ida fiye da yadda ake zato.”

Ya ce a sana’ar gwangwan da suke yi a Gidan Kwali a Ojota akwai tarin matasa ’yan Arewa da ke amfana suna samun abin rufin asiri wanda da dama daga cikinsu ke daukar nauyin iyalai da iyayensu da ’yan uwansu, “Muna da yawa da muke wannan harka ta gwangwan a nan Gidan Kwali, nan ne tushen sana’ar gwangwan a Afirka ta Yamma, kowanenmu yana da akalla mutum 30 da ke aiki kai- tsaye a karkashinsa, to idan muna da irin haka a Arewa za a samu saukin matsalolin da ake fama da su,” inji shi.

Alhaji Ibrahim Soja ya ce dole ne kowa ya fara tunanin yadda zai ba da gudunmawa domin ci gaban yankin da ya fito, domin sai da zaman lafiya ake cin gajiyar arzikin da aka tara, “Kuma dole mu ci gaba da yi wa shugabanninmu addu’a domin ita ce makamin mumini, muna kyautata zato za a kara samun ci gaba mai ma’ana a sabuwar gwamnatin Shugaba Buhari lura da sababbin ministocinsa da wadanda aka sake zaba, muna fata za su dage su yi aiki tukuru domin ci gaban kasarmu da al’ummarta baki daya,” inji shi.