✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Airtel ya samar da layin waya don yaki da mace-macen mata

A sakamakon yawan mace-mace da ake samu na mata masu dauke da juna biyu da kananan yara ’yan kasa da shekara biyar da haihuwa a…

A sakamakon yawan mace-mace da ake samu na mata masu dauke da juna biyu da kananan yara ’yan kasa da shekara biyar da haihuwa a kasar nan, kamfanin waya na Airtel ya hada kai da wata cibiyar Cimma Muradin karni na 2015 a Jihar Kaduna. 

Kamfanin ya ce sun damu matuka ne da yawan mace-macen mata da yara da ke faruwa a karkara a yankin Arewacin kasar nan.
Wannan ne ya sa suka ga ya dace su samar da layin wayan don yaki da mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara a kauyuka hudu da ke karamar Hukumar Ikara.
Shugaban sashen bayar da taimakon kamfanin Mista Chinedo Manjor ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da mata da suka amfana da shirin a Kaduna, ranar Litinin.
Kamfanin Airtel ya kulla kawance ne da cibiyar Cinma Muradin 2015 wato (Pampaida MDG Millennium Project ) da ke aiki a kauyan Pampaida a jihar domin ceto rayukan mata da yara a yankin.
Mista Manjor ya ce kamfanin ta samar da layukan waya kyauta ne ga wasu matasa da mata domin su rika zagayawa gidaje domin binciko marasa lafiya, musamman mata masu juna biyu da yara ’yan kasa da shekaru biyar da haihuwa.
“Manufarmu ta samar masu layukan waya na musamman kyauta a nan, shi ne, mu taimaka wajen rage yawan mace-macen mata da yara jarirai. Wannan zai taimaka musu wajen kiran motocin daukar marasa lafiya da cibiyar ta ajeye a yankin domin daukar marasa lafiya. Wannan ne ya sa muka kulla kawance da wannan cibiya da ke aiki a fannin kiwon lafiya domin cinma muradin karni na 2015 (MDGs) a kauyukan,” inji shi.
Daga nan ya ce sun gayyace manema labarai ne domin su ji bayanai daga wasu daga cikin matan da suka amfana da wannan shiri na kamfanin a kauyan Pampaida a karamar Hukumar Ikara a jahar.
Shima a bayaninsa Kwadinatan Cibiyar Cimma Maradin Karni na shekarar 2015, Dokta Eyitayo Ojo ya ce gwamnatin kasar Japan ce ke daukar nauyin shirin.
Ya kara da cewa akalla suna da ma’aikata da suka kowaya yadda za su rika bi gida-gida suna binciko marasa lafiya domin ba su taimakon da yakamata.
Ya ce inda suke aiki kunkurmin daji ne wanda dole su nemi taimakon wayoyin waya na musamman domin su rike aikawa da sakonnin idan aka samu mara lafiya ko mace mai nakuda dake neman taimako.
Dokta Eyitayo ya kara da cewa baya ga a bangaran kiwon lafiya cibiyar su tare da hadin kan kamfanin Airtel sun taimaka wajen bunkasa harkar noma da fannin samar da ruwan sha da sauransu a kauyuka hudu da suke aiki.
“Akalla a wadannan kauyuka akwai mutane sama da dubu 27 kuma suna da dakunan shan magani hudu ne kacal a kauyan Saulawa da Kwari da Fadama Kale da kuma Pampaida dukkansu akarkashin gundumar Saulawa suke a karamar Hukumar Ikara a Jihar Kaduna,” inji shi.
Roseline Nuhu daya ce daga cikin matan da suka amfana da shirin a kauyen ta kuma yaba wa kamfanin Airtel ne abisa wannan kokari da suke masu na ceton rayukan mata masu juna biyu da kananan yara, ta ce “a gaskiya a yanzu ba wuya da zarar an samu marasa lafiya akwai layin waya da suke kira kyauta domin akai masu dauki.”