✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A’isha Abubakar Hashidu: Ba samun gata ne komai na rayuwa ba

A’isha Abubakar Hashidu, ita ce ’yar tsohon Gwamnan Jihar Gombe Abubakar Hashidu ta farko. Ta rike mukamin Darakta a Kamfanin Azuma Bottling Company da Azuma…

A’isha Abubakar Hashidu, ita ce ’yar tsohon Gwamnan Jihar Gombe Abubakar Hashidu ta farko. Ta rike mukamin Darakta a Kamfanin Azuma Bottling Company da Azuma Inbestment Company da kuma Alind Cabling Company duka a Jihar Gombe. A yanzu ita ce mai ba Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim dankwambo shawara kan ayyukan musamman.

Tarihin rayuwata
Assalamu alaikum, sunana A’isha Abubakar Hashidu, ’yar tsohon Gwamnan Jihar Gombe Abubakar Hashidu. Ni ’yar kauyen Hashidu da ke karamar Hukumar Dukku, a Jihar Gombe ce. Jama’a da yawa ba su san cewa Hashidu gari ba ne, sun dauka sunan mahaifina ne.
Na yi makarantar firamare da ake kira Capital Primary School Yola, a Jihar Adamawa, daga 1979 zuwa 1983. Na kammala Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Yola a shekarar 1989, daga nan na yi Difloma a kwas din Sanin Halayyar Mutanen duniya a Jami’ar Maiduguri, sannan a shekarar 1996 na kammala digirina a kan Kimiyyar Halayyar dan Adam a Jami’ar Maiduguri.  Na yi hidimar kasa daga 1997 zuwa 1998. Daga nan na yi digiri na biyu a kan Huldar Jakadanci da Diflomasiyya a Jami’ar Jos.
Bayan na kammala karatuna ban yi aikin gwamnati ba, kai tsaye na zama darakta kamfanonin mahaifina wadanda suka hada da Kamfanin Azuma Bottling Company da Azuma Inbestment Company da kuma Alind Cabling Company duka a Jihar Gombe, saboda a lokacin ya zama gwamnan Jihar Gombe, don haka ba zai hada dukkan ayyukan a kansa ba.
Daga nan na ci gaba da lura da kamfanonin mahaifina. A yanzu kuma ni ce Mai ba Gwamnan Gombe Ibrahim dankwambo shawara ta musamman kan ayyukan musamman.
Abin da nake tunawa ina karama
Mu takwas ne a wurin mahaifanmu. Mata 5; maza 3. Mun shaku da juna. Mahaifinmu yana tare da mu a dukkan ranakun karshen mako. Nakan tuna da kansa yake daukar mu zuwa sayayya. Nakan kuma iya tuna yadda mahaifiyarmu take lura da mu.
Shakuwa tsakanin iyaye
Na fi shakuwa da mahaifina, shi ya sa ma jama’a suke kira na ’yar lelensa. Akwai kyakkyawar fahimta tsakanina da mahaifiyata. Na fi daukar halayen mahaifina, domin yanzu zai yi fushi, yanzu kuma sai sauko. Yana da yafiya, to haka ni ma nake. Mahaifiyarmu tana da rike abu, za ka rika yi mata abubuwa tana shanyewa.
Burina ina karama
Darasin da na fi so lokacin da nake sakandare shi ne, Geography. Amma dai na fi so in karanta kwas din tsimi da tanadi. Bayan na rubuta jarrabawar JAMB har sakamakon ya fito, sai ya zamana yawan makin din da na samu bai kai in shiga jami’a kai-tsaye ba. Daga nan mahaifina ya ce tun da haka ne, me zai hana in yi difloma, hakan kuwa aka yi, wanda kaddara ta sa na yi difloma a kan halayyar mutanen duniya.
Burina a yanzu
Burina a yanzu shi ne in koyi Faransanci da sauran harsunan duniya, ina da burin yin aiki da Hukumar Lura da Yara ta Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) da kungiyar ba da agaji ta Red Cross. Sannan ina da burin nan gaba in zama lakcara.
Darussan da na koya a rayuwa
Na koyi darussan rayuwa masu yawa, na samu gatan kasancewa da mahaifana, babu abin da na nema na rasa, domin na taso cikin gatan. Amma duk da haka akwai abubuwa masu daci da suka faru da ni, wadannan abubuwan sun ba ni karfin gwiwar tsayawa da kafufuna. Na fahimci ba samun gata ba ne komai a rayuwa. Hakan ya sanya na kara fahimtar yin imani da kaddara.
Yadda na ji bayan na haihu
Na dade kafin in haihu, don haka ba zan iya bayyana hakikanin farin cikin da na ji bayan na haihu ba. Kada ku manta ina da shekara 30 na haihu. Bayan na samu cikin da wata bakwai sai na fara nakuda, hakan ya daga hankalin kowa, a lokacin aka fara tunanin ceto rayuwata, ba ta abin da ke cikina ba. Bayan an yi mini tiyata cikin ikon Allah ni da abin da ke cikina muka rayuwa, wato na samu ’yata ta farko ke nan, yanzu haka tana da shekara 10 da rabi. Shekara daya bayan haihuwar farko, sai na sake samun wani cikin, a karshe na haifi namiji. Yanzu ’ya’yana biyu, kuma su ne farin cikin rayuwata.
Nasarori
Babbar nasarar da na samu ita ce, amincewa da yardar da na samu a wurin mahaifina, sannan a matsayina ta babbar ’yarsa Allah Ya ba ni ikon hada kan dukkan ’ya’yansa, sannan na lura masa da kamfanoninsa yadda ya kamata.   
Yadda nake hada aiki da lura da iyali
Ban samu wata matsala wajen lura da ’ya’yana ba, kasancewar ina tare da ’yan uwana, ko da na fita sukan zauna a wurinsu. Duk lokacin da zan je Gombe yin wani aiki daga nan Abuja, sai in bar su a wurin ’yan uwana, sun saba da su, sai dai su rika kira suna tambayar yaushe zan dawo ne?

kalubale
Babu dan Adam din da zai ce ba shi da kalubale, na fuskanci kalubale mai yawa, kalubalen da ba zan iya bayyanawa ba. Baya ga haka kasancewata mace kuma daga Arewacin Najeriya, akwai abubuwa da dama da aka bar mu a baya, ta kai a lokacin da nake kan hanyar zuwa gida ne na ga wadansu mata kanana dauke da fartanya za su je gona, bayan na koma gida muna tattaunawa sai ake fada mini talauci ne ya sanya haka, wannan al’amarin ya daga mini hankali, domin na rika tambayar kaina me ya sa ba sa zuwa makaranta? Mun tattauna da kannena mata, mun kuma yanke shawarar za mu shiga kauyuka don mu gano dalilin da ya sa ba sa zuwa makaranta, sannan mu taimaka.
A yanzu ina shirye-shiryen kaddamar da wani shirin da zai taimaka wa mata da yara, shirin da nake burin ya tsaya da kafafunsa har fiye da shekara 10.
A yanzu haka ina da burin taimaka wa mata masu yoyon fitsari, wanda hakan yana faruwa ne saboda rashin wayar da kan mata. Akan aurar da mata masu karancin shekaru, inda kuma ba su san yadda za su lura da kansu ba, bayan sun kamu da ciwon yoyon fitsari kuma sai a guje su, a rika hantarar su. Ba za su iya wani aiki ba, saboda halin da suka samu kansu a ciki. Sannan jama’a da dama ba su mayar da hankali wajen fahimtar yadda ciwon yake ba.  
Yadda nake hutawa
Ban cika damun kaina don in je nan da can ba, idan ba na komai wani lokacin nakan yi kwana biyu a cikin dakina, inda nakan yi karance-karance da kuma kallace-kallacen tasoshin talabijin don ganin halin da duniya take ciki.
Abin koyi
Mahaifina shi ne wanda nake koyi da shi.
Abin da yake sanya ni farin ciki
Babu abin da ya fi ba ni farin ciki kamar iyalina. Akwai lokacin da wani abu ya faru da ni, sai na shiga daki ina kuka, bayan ’ya’yana sun shigo daki sun gan ni ina kuka ne, sai suka fara kuka, abin ya ba ni mamaki, na tambaye su me ya sa suke kuka, sai suka ce don sun ga ina kuka ne, hakan ya sanya na fara dariya, su ma sai suka fara dariya. Daga nan na koyi darasin mutum ya daina kuka a gaban ’ya’yansa.
Tufafi
Na fi so in yi shiga ta mutunci, kada ku manta ni Musulma ce, don haka ba na son yin shigar da za ta zubar mini da kima.