✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aishatu Jibrin Dukku: ’Yar Majalisar Tarayya ta tallafa wa mata 300 a Gombe

Ba zan bai wa al'umma kunya ba a Gombe kamar yadda muke ayyukan haka za mu ci gaba.

’Yar Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Dukku da Nafada a Jihar Gombe, Hajiya Aishatu Jibrin Dukku, ta raba wa Mata 300 tallafin jari a mazabarta.

Aishatu Jibrin Dukku, ta ce wannan rana ce ta musamman a wajen ta domin nuna kulawa ga mata da kuma kaunar gwamna bisa ayyukan raya kasa da yake yi a jihar wanda ita ma ta yi amfani da ranar ta tallafawa Mata.

Ta yaba wa gwamna Muhammad Inuwa Yahaya kan yadda ya gina musu gadar da ta karye da ta hade garuruwan Dukku da Nafada.

Ta ce ta san gwamnan mai kishin al’umma ne wanda yake tabbatar da ganin romon dimokuradiyya ya kwarara a ko’ina fadin jihar musamman a yankin mazabarta na Dukku da Nafada.

A cewarta, bisa ga ayyukan da ya yi, a zaben shekarar 2023 da ke tafe za su saka masa wajen ganin ya zarce a karo na biyu, tana mai kira ga matan da su mallakin katin zaben domin dangwala masa kuri’unsu.

“Ku fito ku yanki katin zabe domin zaben wanda ya cancanta ya jagorance ku,” inji Aisha.

’Yar Majalisar ta kuma yi kira ga gwamna Inuwa da ya ninka adadin Matan da ake tallafawa a gwamnatinsa domin su suka fi shan wahala a lokacin zabe.

Da yake jawabi, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ya jinjina wa kokarin ’Yar Majalisar kan yadda take kawo wa mazabarta ayyukan ci gaba.

Ya ce kamar yadda Aishatu Jibrin Dukku, take taimakawa Mata shi ma a gwamnatinsa an shigar da mata sosai da suke rike da manyan mukamai.

Ya ce daga hawan ’yar majalisar wannan ne karo na uku da take tallafa wa mata da matasa a mazabunta.

“Ba zan bai wa al’umma kunya ba a Gombe kamar yadda muke ayyukan haka za mu ci gaba,” a cewarsa.

A nata tsokacin, uwargidan gwamnan, Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, ta ce Mata su ne ginshikin kowane gida don haka wannan tallafi da aka basu su ririta shi don ya amfane su ya amfanar da wasu.

Asma’u ta ce Aishatu Jibrin Dukku ta bai wa Mata dari 300 tallafi naira dubu 10 kowacce da nufin bunkasa sana’ar su – wacce ba ta da jari kuma ta samu, wanda idan suka ririta shi sun samu hanyar dogaro da kai.

Wasu daga cikin matan da suka samu tallafin da suka zanta da wakilin mu sun gode wa Aishatu Jibrin Dukku, bisa wannan tallafi inda suka mata fatan alheri.