✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’adar Bahaushe jiya da yau

Shi dai Malam Bahaushe a bisa tarihin da ya shude, mutum ne baki sosai, mara tsawo, mai shafaffen hanci da faffadan baki. Amma dai wannan…

Shi dai Malam Bahaushe a bisa tarihin da ya shude, mutum ne baki sosai, mara tsawo, mai shafaffen hanci da faffadan baki. Amma dai wannan siffantawar ta Bahaushe a kan iya cewa tana daf da a kirata tarihi, bisa ga yadda aka samu auratayya sosai tsakanin kabilar Hausawa da sauran kabilu daban-daban. Al’ummar Hausawa mutane ne da suka shahara a kan riko ga dabi’u da al’adunsu na gargajiya. Sai dai canji da suka samu na addini wanda a fari suka wanzu cikin addinin gargajiya da aka fi sani da Maguzanci, sannan daga bisani suka rungumi addininin Islama. Ga Malam Bahaushe, babu wani abu da ya dara addininsa martaba da kima.

Hausawa sun bambanta da sauran kabilun Najeriya, ta hanyar tsananin rukonsu ga al’adun tufafin sawa  da abinci da gine-gine da sauransu. daukacin Hausawa za ka same su rungume da al’adunsu. Ba ma iya Bahaushen kasarmu Najeriya ba, har da sauran Hausawan wasu kasashen daban.

A JIYA, Malam Bahaushe ba ya iya cin abincinsa na dare shi kadai a gida. Sai dai ya ci abincin tare da sauran makwaftansa. Kowa  zai fiddo da abincinsa, yawanci tuwo da miyar kuka su zauna cikin da’ira, suna ci kwano bayan kwano cikin annashuwa, har kowa ya koshi. Idan kuma an samu saura bayan sun koshi sukan tattara su bai wa almajirai wadanda akasari suke rabewa a wajen domin ko sa dan samu saura, su ma su kashe yunwar cikinsu. Wannan al’adar ita ake yi wa lakabi da ‘Ciyayya’ ma’ana dai cin abinci tare da abokan arziki. Idan kuma cikin rashin sa’a akwai wani da ranar Allah bai yassare masa karfin iya fiddo da tuwon ba, hakan ba zai hana shi zuwa a ci tare da shi ba. Wannan ma shi zai sanya abokan nasa su fuskanci yanayin rashi ko matsi da ke fuskantarsa. Idan ma ya jima cikin halin matsin rayuwa, to sauran mutanen da suke taren za su tallafa masa da ‘yan kayayyakin abinci da na masarufi. Kuma idan wani ne daga cikinsu ya dauki ‘yan kwanaki biyu bai samu halartar ciyayyar ta su ba, to sauran fa ba za su yi kasa-a-gwiwa ba wajen  tuntuba a game da shi ba. Wasu har ma ba za su samu nutsuwa ba sai sun aika gidansa ko wajen mai-dakinsa. Idan ba shi da lafiya ne ko kuma wata matsala ta rayuwace ke damunsa, to za su yi yunkuri ba shi tallafi da addu’o’i daya bayan daya ko kuma a kungiyance.

A JIYA, Budurci na ‘yan mata yana da matukar martaba. Kusan duka ‘yan matan Hausawa suna rike diyancinsu har a yi musu aure. Rasa diyancin ‘ya mace budurwa tamkar rasa rai ne. Wannan ita ce babbar fitina ga rayuwar yarinya kafin a yi mata aure. Ana gudanar da wani bincike na al’ada domin tabbatar da budurcin ‘ya mace kafin a kai ta dakin aure. Idan kuma aka samu yarinyar ba ta kai budurcinta ba, to za ta rasa rayuwarta nan take. Idan kuma wasu dalilai suka sanya ba a yi binciken ba har amaryar ta kwana a dakin mijinta, kuma daga bisani angon ya gano cewar ba ta tsira da budurcinta ba, to wannan sabon auren dai za a warwareshi. Kafin warwarewar auren, ‘yan uwan angon mata sukan ziyarci dakin amarcin dan uwan ango washegarin tarewar amarya, domin tabbatar da shin surikarsu ta tsira da budurcinta kafin auren? Sukan nutsuwa su saka ido domin nazarin wata alama duk kankantarta da ka iya tabbatar musu da amaryar nan kamammiya ce. Misali a ce sun ga wani fasasshen faranti, ko wata kwarya, wadda angon ya fasa domin ya tabbatar da budurcin amaryarsa ga duk wani bako da ka iya zuwa domin nazarin amaryar sa. Idan kuma bakon ya gaza ganin wata alama, yakan yi wa amaryar wata ‘yar hikima ta hanyar sanya ta ta kawo masa ruwa. Wanda a galibi a kwarya suke kawo ruwan. Idan suka amshi ruwan sannan suka yi nasarar ganin tsaga ko ‘yar karamar kofa a jikin kwaryar, to kuma duk wani kokonto ya kau. Amaryar ba ta tsira da budurcinta.

A JIYA, yawancin Hausawa ba su san soyayya kafin aure ba. Amma galibi auraren da ake dacen samun wanzuwar soyayya kafin su, to tattaunawa tsakanin saurayin da budurwar tana wakana da dare. Saurayin wanda yake samun rakiyar babban abokinsa sukan tura yaro karami gidan su budurwar domin ya kira musu ita su yi hira. Wannan wata al’ada ce da ake gudanarwa da dare. Kuma Hausawa suna yi mata lakabi da ‘zance’. ‘Ta na zuwa’ yawanci dan aiken yake sanar da su bayan ya sanar da ita zuwansu. Shi kuma gogan na ta yakan bai wa yaron tukwicin ‘yan kwabbai, domin nuna yabawa da kan-gadon dan aikensa. Cikin farin ciki yaron zai amsa daga bisani ya ruga gida baki har kunne. 

Zancensu kacokan suna aiwatar da shi cikin tsananin kunya da kamun kai. Suna zama can nesa da juna, sannan yarinyar takan gaza iya furta komai ga saurayinta, domin tsananin kunya. Sai dai ta rika gyada kai, ko girgiza kai, a yayin da fuskarta ke fuskantar kasa tana kallon kasan. Bahaushiyar da sam ba ta iya amsar kudin zance ba. Ma’ana ’yar kyautar kudin da saurayin zai ba ta lokacin da ya zo zance. Zai yi iya yinsa domin ta amsa, amma sam ba ta iya karba. Wannan ba komai ba ne face tsananin kamun kai da kunya da ke cikin al’adun Hausawa. karshe dai ba yadda zai yi sai dai ya aje ’yan kudin a gefenta. Ita ko ba za ta iya dauka ba sai bayan saurayin da abokinsa sun shuri takalmansu sun tafi. 

Auren hadi ko na dan dangi yawanci shi ne auren da Hausawan suka fi yi. Cikin ikon Allah kuma suna zamowa aure mai inganci cike da zaman lafiya. Ana daukar lokaci mai tsawo ba ka ji wata husuma ta bullo a tsakanin ma’auratan ba. 

Halayyar auratayyar Hausawa da rikon aure a zamanin da, da kuma kauna da son juna da sauran su, za a iya kamanta ta da karim maganar Hausawa da take cewa ‘Naka naka ne ko ya ci namanka ba zai tauna kashin ba’

Hausawa ke nan a wancan zamanin. Amma a wannan zamanin, mukan iya cewa labarin ya sauya salo mutuka gaya. Kamannin da aka san su da Malam Bahaushe su ma mukan iya cewa sun sauya. Kamar siffa da kyawunsu, duk da dai an ce shi kyau yana daga cikin idon mai hangensa. Wannan sauyin kuma ba komai ba ne ya kawo shi face auratayya da ta shiga tsakanin Hausawa da sauran kabilu, kamar Fulani da Nufawa da Barebari da sauransu. Amma auratayyarsu da Fulani ta fi kowacce tasiri da karfi da har ta kai yanzu ‘yan jarida suke kiransu da sunan ‘Hausa-Fulani.’ 

A yanzu muna iya cewa al’adar ciyayya ta yi batan-dabo a cikin al’dun Hausawa. Wasu daga cikin ‘yan-matan Hausawa marasa aure sun fara sakin turbar da aka san su da bi. Abin takaici, wasu ana yaudararsu da kudi ko kyale-kyalen duniya domin a kawar da budurcinsu kafin aurensu.

A YAU Hausawa sun dauki dabi’ar sakin matansu a kan ‘yan matsalolin cikin aure da za a iya kawar da kai gare su, ko kuma a samo masalaha cikin ruwan sanyi. Daga bisani kuma ya bar ‘ya’yan ita wadda ya saka din a hannun kishiyoyi. Yin hakan kuma ba komai ya ke haifarwa ba face jefa rayuwar yaran a matsanancin kunci, domin gallazawar da yaran suke sha a hannun matan mahaifinsu yawancin lokuta. Wasu kuma matasan abin mamaki sai ka ga sun share shekaru da dama cikin tsananin soyayya, amma sai su gaza kamanta irin shekarun nan da suka yi na soyayya a cikin rayuwar aurensu. Cikin lokaci kalilan sai ka ji igiyar auren ta katse.

A YAU, shagulgula kamar liyafa, yanka kek da bidiri iri-iri domin gudanar da bikin aure su ne abin da Hausawa suka fi lale da shi. Ba da jimawa ba muka samu labarin wani ango da ya mula ya makawa amaryar tasa saki a ranar daurin aurensu. ‘Yan mintuna kadan da a kai masa amaryar dakin amarcinsu. Ba kuma komai ya jawo sakin ba face labarin da ya same shi na gudanar da wata liyafa da amaryar take yi, wanda wani tsohon saurayinta ya dauki nauyin hada mata. Kuma tun fil-azal angon ya nuna kin amincewa da hakan.

A YAU, matasan Hausawa sun ari al’adar sabule wando (earth down), ko saka tsukakken wando (pensil), ko askin iskanci irin na shahararren dan kwallon nan mai lakabin Balatoli da dai sauran kyale-kyalen zamani. Wani ya yi ma da bai jima sosai da shudewa ba, shi ne wata sabuwar rawa da ake yi mata lakabi da ‘Dab,’ wadda wani mawaki ya shigo da ita kasar nan mai suna Olamide. Ita dai rawar Dab an somata kusan shekara shida baya ko kuma kwatankwacin hakan. Kamar dai yadda mawakin gambaran nan na kasar Amurka wato Bow Bow ya fadi, ita rawar Dab ta samo asali ne daga al’ummar Kannabis. Wannan sahi ne sabon salo yayi ga matasan Hausawa.

A YAU, wasu Hausawan sun dauki halayyar nuna raini ga ‘yan-uwansu da ke karantar harshen Hausa a jami’o’i da sauran makarantun gaba da sakandare. Idan kuma ka ce su rubuta sakin-layi guda daya da harshen Hausa, da yawansu ba za su iya rubutawa daidai ba. Turawa da Larabawa da da sauransu,  duk suna karantar harsunansu cikin alfahari da tunkaho!

Shahararrun mutane kamar Malami-uban-malamai, Farfesa dandatti Abdulkadir da Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya da Farfesa M.K. Galadanci da Farfesa Abdulkadir Dangambo, Farfesa Abdalla Uba Adamu da sauransu za’a iya rubuta su a jikin zinare a matsayin shahararrun masana, kuma jigogi a fannin ilmi da nazarin harshen Hausa a kasarmu Najeriya da sauran sassan duniya.

karshe dai an san cewa tabarbarewa da wancakali da al’adu masu kyau na gargajiya ba a iya kabilar Hausawa ya tsaya ba. Sauran kabilun kasar nan su ma suna fama da irin wannan matsalolin, ko ma fiye da hakan. A takaice dai za mu iya cewa wannan matsala ce da ta shafi duk wani sashi na duniya, sakomakon sauyin zamani. Hausawa ma ba su fiye wancakali da al’amuran al’adu masu kyau ba kamar wasu kabilun. Za mu iya cewa kabilar Hausa tana daya daga cikin mafi kyawun kabilu a Najeriya da ma Afirka gaba daya! Idan ka dubi Hausawan zamani, za ka amince da karin maganar Hausawan da ta ke cewa ‘Bahaushe mai ban Haushi.’ Amma dai Bahausahe ya yi gaskiya da ya ce: KOWA YA BAR GIDA: GIDA YA BAR SHI!! 

(Yasir Kallah ne ya fassara makalar Bello Sagir, da fita a Dailytrust ta 16 ga Agustan 2017, Shafi na 42. BELLO SAGIR [email protected]) 08132518714.