✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alaka da barayi: Yadda wadansu hakimai suka yi asarar rawunansu a Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ba da sanarwar sauke hakimai biyu da dakatar da biyu daga kan kujerunsu saboda zarginsu da alaka da ’yan bindigar da…

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ba da sanarwar sauke hakimai biyu da dakatar da biyu daga kan kujerunsu saboda zarginsu da alaka da ’yan bindigar da suka addabi jihar.

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar, Alhaji Bello Dankande Gamji ne ya ba da sanarwar a wani taron manema labarai da ya gudana a Gusau, babban birnin jihar.

Kwamishinan ya ce babu wani mai rike da sarautar gargajiya da gwamnati za ta saurara mawa muddin aka same shi na yi wa sha’anin tsaron jihar zagon kasa.

Hakiman da abin ya shafa su ne na Ruwan Gora da ke Karamar Hukumar Bukkuyum, Alhaji Is’hak Sadik da na Gwalli da ke Karamar Hukumar Gumi, Alhaji Musa Gwalli.

Haka kuma akwai Hakimin Gyadu da na Tungar Dutse, wadanda aka dakatar da su kuma an riga an fara bincike a kan alakarsu da ’yan bindigar.

“Gwamnati a shirye take ta ga cewa an ga bayan ’yan ta’adda a wannan jiha, don haka ne ma muka umarci shugabannin kananan hukumomi su mai da hankali wajen kashe kudadensu kan sha’anin tsaro, maimakon wani abu daban.

“Mun fada masu cewa duk abin da jami’an tsaro da ke aikin kakkabe ’yan ta’adda a kananan hukumomin nasu suke bukata, to su samar da shi. Kai mun fada masu cewa in ban da sha’anin kiwon lafiya da ilimi da kuma samar da ruwan sha, to kada su kashe kudadensu a kan komai in ba sha’anin tsaro ba,” inji Kwamishinan.

Dankande ya kara da cewa, tun daga kan sarki zuwa hakimi zuwa dagaci da  mai unguwa, wanda aka samu da kulla alaka da ’yan ta’adda zai yi asarar rawaninsa kuma ya fuskanci shari’a, ba da  bata lokaci ba.

Binciken da Aminiya ya gano cewa hakiman da aka ambata, ana zarginsu da alaka da ’yan bindigar da suka addabi jihar. Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa; yadda aka ga wani hakimi yana hulda da wadansu daga cikin wadanda jama’a ba su yarda da dabi’arsu ba ya sa mutane suka sanya alamar tambaya a kansa kuma suka sanar da hukumomi kafin a dauki mataki a kansa.

Har zuwa hada rahoton nan, dukan hakiman suna hannun jami’an tsaro domin amsa tambayoyi don gano hakikanin abin da ya faru. “Da ma an dade ana zargin masu rike da sarautun gargajiya a jihar da yin zagon-kasa ga sha’anin tsaro. Suna kasafi na shanun sata da kuma hada kai da masu laifi don biyan bukatun kansu,” inji shi.

Amma wani jami’in ma’aikatar ta kananan hukumomi da lamuran masarautu ya shaida wa wakilinmu cewa har yanzu zargi ne kawai ake musu kuma bincike shi zai tabbatar da laifinsu ko kuma akasin haka.

To sai dai akwai masu ganin cewa a wasu lokutan alaka a tsakanin masu rike da sarautun gargajiya da ’yan bindigar ta dole ce.

“Wasu lokutan za ka ga cewa wadansu dagatan suna zaune a garuruwan da su ’yan bindigar suka yi wa kawanya kuma babu yadda za su yi su ki yi musu biyyaya don gudun abin da zai biyo baya,” inji Sani Kadima, wani mazaunin wani kauye.

“Kai akwai ma hakiman da ke karbar umarni a wurin ’yan bindigar maimakon sarakuna. Wannan kuwa bai rasa nasaba da yadda suke gudun abin da zai biyo baya daga ’yan bindigar. Akasarin wadannan wurare za ka ga cewa babu jami’an tsaro, don haka su ’yan bindigar ke cin karensu ba babbaka,” inji shi.

Ko a watan Yulin da ya gabata, Hakimin Kucheri, a Karamar Hukumar Tsafe ya rasa ransa, bayan da ’yan bindigar suka harbe shi a gidansa.

Rohotanni sun ce ya yi wasu maganganu ne a wurin wani taro kan sha’anin tsaro, wanda kuma aka samu wani ya tsegunta wa ’yan bindigar; suka kuma zo suka hallaka shi.