✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alhazai biyu na Jihar Sakkwato sun dawo da Dala 700 da suka tsinta

Mahajjata biyu daga Jihar Sakkwato sun dawo da kimanin Dala 700 da Saifa dubu 15 da kuma Riyal 137 da suka tsinta na wani Mahajjaci…

Mahajjata biyu daga Jihar Sakkwato sun dawo da kimanin Dala 700 da Saifa dubu 15 da kuma Riyal 137 da suka tsinta na wani Mahajjaci daga jihar.
Daya daga cikin mahajjatan, Dauda Ibrahim daga Karamar Hukumar Gwadabawa ya ce sun tsinci kudin ne a hawa na biyu na otel din Rhoda da ke Unguwar Masfalah inda aka sauke mahajjatan jihar.
Ibrahim wanda manomin albasa ne ya fada wa Aminiya cewa duk irin mawuyacin halin da yake ciki, ba zai sa ya zama mai hadama ba.
Daya daga cikin kwamitin malaman jihar, Shaik Umar Maidamma Shagari ya yaba wa mahajjatan saboda kokarin da suka yi inda ya basu tabbacin cewa Allah zai saka musu.
Ya ce Kwamitinsu ya gano tare da mika kudin ga mai su mai suna Shu’aibu Usman daga Karamar Hukumar Isa.