✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aljeriya ta dakatar da gasar rukuninta bayan an kashe wani dan kwallo

Hukumar shirya kwallon kafa ta Aljeriya a ranar Litinin da ta gabata ne ta sanar da dakatar da gasar rukunin kasar bayan da aka samu…

Hukumar shirya kwallon kafa ta Aljeriya a ranar Litinin da ta gabata ne ta sanar da dakatar da gasar rukunin kasar bayan da aka samu rahoton mutuwar dan kwallon JS Kabylie mai suna Albert Ebose dan asalin Kamaru bayan da wani dan kallo ya jefe shi da dutse a ka al’amarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Hukumar kwallon kafa ta kasar ta ce ta dauki matakin dakatar da gasar ce bayan ta gudanar da taron gaggawa a kan al’amarin a ranar Lahadin da ta wuce.
Sashen wasanni na kafar sadarwar BBC ya ce, Albert Ebose, dan kimanin shekara 24  ya gamu da ajalinsa ne jim kadan bayan an tashi wasa a tsakanin kulob dinsa na JS Kabylie da kuma na USM Alger a ranar Asabar da ta wuce inda kulob din JS Kabylie ya sha kashi da ci 2-1.  Hasalima marigayin ne ya jefa kwallo daya da kulob din nasa ya zura a ragar USM Alger.
Jim kadan bayan an kammala wasan ne a hanyarsa ta fita daga filin wasan da ake wa lakabi da 1st Nobember 1954 wani dan kallo ya jefe shi da dutse a ka al’amarin da ya sa ya zube kasa a sume kuma aka garzaya da shi asibiti.  Kwana biyu da kwantar da shi ne rai ya yi halinsa.
Tuni gwamnatin kasar ta bayar da umarnin a rufe filin wasan sannan Shugaban Hukumar shirya kwallon kafa a Afirka (CAF) Issa Hayatou ya bayar da umarnin gudanar da bincike a kan al’amarin don zakulo wanda ya aikata wannan danyen aiki don a hukunta shi.
Marigayin ya yi wasa a kasashen Turai da dama da suka hada da Rasha da Beljiyam da Fotugal kafin daga bisani ya koma Aljeriya a shekarar bara don cigaba da yin kwallo.