✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alkalan wasa ne matsalar wasan kwallon kafa a Najeriya – Kocin Kano Pillars

An zargi wasu daga cikin alkalan wasa da kokarin kashe wasan  kwallon kafa musamman gasar rukunin firimiya ta Najeriya bisa yadda kiri-da- muzu suke hura…

An zargi wasu daga cikin alkalan wasa da kokarin kashe wasan  kwallon kafa musamman gasar rukunin firimiya ta Najeriya bisa yadda kiri-da- muzu suke hura yadda zuciyarsu ta raya masu.

Babban mai horar da kungiyar wasan kwallon kafa ta Kano Pillars Ibrahim Musa ne ya furta haka yayin hira da Aminiya, a Kalaba jim kadan da kammala fafatawar da kungiyar ta yi da takwararta ta Enyimba Aba a ranar Lahadin da ta gabata.

Duk da kasancewa kungiyar Kano pillars ta yi wasa mai kayatarwa a filin wasa na U.J Esuene , an tashi wasan ne kulob din Enyimba na da ci daya mai ban haushi.

daruruwan ’yan kallo ba su samu damar shiga filin ba sai da aka koma hutun rabin lokaci saboda yadda mahukunta suka bayar da umarnin kada a bar wani ko wasu su shiga don a samar da cikakken tsaro.

Bayan an bude kofofin shiga filin wasan ne jama’a da dama suka yi tururuwar shiga ciki har da wadanda suka sayi tikiti da kuma ’yan alfarma.

Koci Musa ya ci gaba da cewa: “ka ga yadda alkalan wasa ke kashe wasan kwallon kafa a Najeriya ta hanyar murde gaskiya suna hura wasa yadda suke so, gaskiya ban cika son yin magana a kan alkalan wasa ba amma dubi yadda wannan alkalin wasa ya yi mana magudi kuma hakan ke kashe karsashin wasan kwallon kafa a kasar nan.”  

Alkalin wasan ya hura son ransa ne, don akwai damar da muka samu na fanshe kwallon da Enyimba ta zura a ragarmu amma sai alkalin wasan ya dakile.

Ya ce duk da haka Kano Pillars za ta yi kokarin ganin ta gama a daya daga cikin kungiyoyi hudun da za su kasance a saman teburin gasar ta bana, duk da irin magudin da alkalan wasan ke yi musu.

Daga nan ya hori magoya bayan kungiyar su kwantar da hankalinsu kuma su ci gaba da marawa kungiyar baya a duk lokacin da take yin wasa a ko’ina a kasar nan.