✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alkur’ani ne maganin matsalolin kasar nan – Mataimakin Gwamna

An bayyana Alkur’ani Mai girma a matsayin maganin duk matsalolin da ake fuskanta a kasar nan. Wannan jawabi ya fito daga bakin Mataimakin Gwamnan Jihar…

An bayyana Alkur’ani Mai girma a matsayin maganin duk matsalolin da ake fuskanta a kasar nan.

Wannan jawabi ya fito daga bakin Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa kan ayyuka na musamman, Idris Salisu Rogo, a ranar Alhamis din makon jiya, lokacin bude musabakar Alku’ani a tsakanin makarantun sakandaren ’yan matan da ba na Arabiyya ba, da kungiyar Kula da Karatun Alkur’ani ta kasa (Rabida) ta shirya da hadin gwiwar Kwalejin ’Yan Mata ta Zahra Nanono da ke Kano.
Farfesa Hafiz Abubakar wanda kuma shi ne Kwamishinan Ilimi na Jihar, ya ce: “Matukar jama’a za su koma su rungumi Alkur’ani tare da yin aiki da abin da yake koyarwa, babu shakka za a samu maganin matsalolin da ake fuskanta a kasar nan. Malamai suna gaya mana cewa Alkur’ani waraka ne ga dukan cututtukan da suka hada da na jiki da zuciya. Haka kuma kariya ne ga dukkanin bala’o’i da musibu da dan Adam ka iya cin karo da su a rayuwa.”
Mataimakin Gwamnan ya nanata cewa gwamnatin Jihar Kano a shirye take ta ci gaba da bayar da duk wani taimako ga makarantun da ke jihar, musamman wadanda ke kokari wajen yada addini da ciyar da karatun Alkur’ani gaba.
Tunda farko a jawabin maraba, Shugaban kungiyar Rabida, Malam Shu’aibu Shehu ya ce wannan shi ne karo na hudu da kungiyar tare da hadin gwiwar Kwalejin ’Yan Mata ta Zahra Nanono ke shirya irin wannan musabaka a tsakanin makarantun sakandaren mata da ke kasar nan da nufin zaburar da dalibai wajen karatun Alkur’ani tare da cusa kayawawan dabi’u a zukatan daliban. “Muna shirya wannan musabaka ne don cusa wa daliban kyawawan dabi’u ta hanyar koyi da Alkur’ani, ta yadda za a samar da iyaye nagari a nan gaba. Haka kuma muna kokarin samar da hadin kai tsakanin daliban da ke kasar nan,” inji shi.
Shi ma a jawabinsa, Daraktan Kwalejin ’Yan Mata ta Zahra Nanono, Alhaji Umar Nuhu Wali ya tabo tarihin shirya wannan musabaka ce, inda ya ce kimanin shekara 30 mai makarantarsu wato marigayiya Hajiya Zahra Nanono ta fara shirya musabakar Alkur’ani a tsakanin makarantu; wanda daga nan ne Jami’ar Usman danfodiyo ta yi koyi da ita, inda ita ma ta fara shirya musabakar a fadin kasar nan.
Ya yi kira ga daliban da suka shiga musabakar su dauki kansu a matsayin masu nasara koda kuwa sakamakon musabakar bai nuna su ne kan gaba ba. “A wurinmu, duk dalibar da ta zo wurin nan mai nasara ce, domin babu nasara a rayuwa da ta kai darajar karatun Alkur’ani. Haka muna kira ga dalibai su rika koyi da koyarwar Alku’ani a cikin mu’amalolinsu na yau da kullum.”
Makarantu da dama ne suka shiga musabakar da suka fito daga jihohin Jigawa da Kaduna da Katsina da Zamfara da Borno da Nassarawa da Oyo da Bauchi da Birnin Tarayya Abuja da kuma mai masaukin baki, Jihar Kano.