✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah bai yi kuskuren samar da Najeriya ba – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ’yan Najeriya su gode wa Allah da Ya tattara Ya hada su a matsayin kasa daya al’umma daya. Shugaba…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ’yan Najeriya su gode wa Allah da Ya tattara Ya hada su a matsayin kasa daya al’umma daya.

Shugaba Buhari ya fadi haka ne a ranar Litinin lokacin da yake karbar Babban Jagoran Cocin Deeper Life, Fasto William Kumuyi a fadarsa da ke Abuja. “Allah bai yi kuskure wajen samar da Najeriya mai kabilu fiye da 250 ba, sannan Ya hada su waje guda da ake kira Najeriya,” inji Shugaba Buhari.

“Don haka wajibi ne mu gode wa Ubangiji wajen tara mu waje guda. Saboda Yana sane da abin da Yake yi. Bai yi kuskure ba wajen yin haka,” inji shi.

Da yake siffanta kasar a matsayin wata kasa ta musamman da Allah Ya yi mata arzikin yawan jama’a da yalwatattun ma’adinai, sai Shugaban Kasar ya ce: “Muna da kalubale a gabanmu wajen fahimtar da al’ummarmu wannan darasi har sai sun gane haka. Ina zaton bisa kwarewar da na samu a matsayin Gwamna da Ministan Man fetur da kuma Shugaban Kasa na soja sannan da Shugaban Asusun Rarar Kudin Man fetur (PTF), na ga wadannan abubuwa duka a zahiri, don haka Najeriya tana da dukan damar da za ta tsaya a kan kafafunta.”

Ya kara da cewa, “Na samu zarafin tunawa da hakan sakamakon ziyarar nan taka. Kuma ina godiya matuka.”

Shugaba Buhari ya bayyana Fasto Kumuyi a matsayin jajirtacce mai fasaha wanda ya shafe lokaci mai tsawo yana karantarwa a jami’a gabanin ya dukufa cikin hidamar Allah. Sannan ya gode masa bisa karbar gayyatar Fadar Shugaban Kasa don yin huduba ga al’umma a ranar Bikin Cikar Najeriya Shekara 58 da samun ’yancin kai.

A jawabinsa tun farko, Fasto William Kumuyi, ya bayyana karbar da Shugaban Kasa ya yi masa tare da ayarinsa a matsayin abin alfahari gare shi, musamman idan aka yi la’akari da irin dawainiyoyin da wannan rana ta 1 ga Oktoba ta kunsa.

Kuma ya jinjina wa Shugaban Kasa bisa namijin kokarinsa wajen mai da Najeriya kan turbar da ta dace yana mai cewa: ”Ina rokonka da ka daure kuma ka ci gaba da wannan fafutika wajen yin abin da ya dace. Hakika ba kowa ne zai mara maka baya a bayyane ba, amma mu muna yi maka addu’ar samun nasarar mulkin nan da Allah Ya ba ka domin ciyar da kasarmu da al’ummarmu gaba.”