✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amintacce da mugun mutum

Mugun mutum yakan gudu, alhali kuwa ba mai korarsa, amma amintaccen mutum kamar zaki yake, ba ya da tsoro. Al’umma za ta karfafa ta jure…

Mugun mutum yakan gudu, alhali kuwa ba mai korarsa, amma amintaccen mutum kamar zaki yake, ba ya da tsoro. Al’umma za ta karfafa ta jure idan shugabanninta masu basira ne, masu hankali. Amma idan kasar mai aikata zunubi ce za ta samu shugabanni da yawa. Mai mulki wanda yake zaluntar talakawa, ya zama kamar ruwa mai lalatar da amfanin gona. Wanda ba ya bin doka tare da mugaye yake, amma idan kana bin doka kai abokin gaban mugaye ne. Mugaye ba su san gaskiya ba, amma wadanda suke yi wa Ubangiji sujada sun san ta sosai. Gara ka zama matalauci mai aminci da ka zama mawadaci, marar aminci. Saurayi wanda ya kiyaye doka mai basira ne shi, amma wanda yake abuta da ’yan iska zai zama mai jawo wa mahaifinsa kunya. Idan kana tara dukiya ta wurin ba da bashi da ruwa kana kuma kwarar jama’a, dukiyarka za ta koma ga wanda yake yi wa talakawa alheri. Idan ka ki biyayya ga doka, Allah zai ki jin addu’o’inka. Idan ka yaudari mutumin kirki don ya fada cikin mugunta, kai kanka ne za ka fada cikin tarkon da ka haka. Marar laifi kuwa zai samu babban sakamako. Attajirai a koyaushe zato suke su masu hikima ne, amma matalauci mai tunani ya fi sanin abin da yake daidai. Sa’ar da mutanen kirki suke sarauta, kowa da kowa yakan yi biki, amma sa’ar da mugaye suka kama mulki mutane sukan rika buya. Ba za ka taba cin nasara a zamanka ba muddin kana boye laifuffunka. Ka furta zunubanka ka tuba, sa’an nan Allah zai yi maka jinkai. Mutumin da yake tsoron Ubangiji koyaushe, zai yi farin ciki, amma idan ya taurare zai lalace. Talakawa ba su da wani taimako sa’ar da suke karkashin mulkin mugu. Abin tsoro ne shi kamar zaki mai ruri, ko beyar mai sanda. Mai mulki wanda ba ya da basira yakan zama mai mugun tsanani. Amma wanda yake kin rashin aminci, ko ta kaka zai dade yana mulki.Mutumin da yake da laifin kisan kai, yana haka wa kansa kabari da gaggawa. Kada ka yi kokarin hana shi. Ka yi aminci za ka zauna lafiya, idan kuwa ka yi rashin aminci za ka fadi. Manomin da yake aiki sosai, zai samu wadataccen abinci, amma mutanen da suke zaman banza koyaushe, za su zama matalauta. Amintaccen mutum zai cika kwanakinsa lafiya, amma idan kana so ka samu dukiya dare daya, za a hukunta ka. Nuna son kai mugun abu ne, wadansu alkalai sukan aikata mugunta saboda ’yar karamar rashawa. Mutum mai hadama yana gaggawar samun dukiya, bai kuwa sani ba, ashe, fatara ce za ta same shi. Wanda ya tsawata wa mutum zai samu yabo daga baya, fiye da wanda ya yi masa dadin baki. Wanda yake yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa sata, yana kuwa tsammani ba laifi ba ne, daidai da barawo yake. Mutum mai hadama yana haddasa tashin hankali, amma wanda ya dogara ga Ubangiji zai samu wadar zuci. Wanda yake dogara ga son zuciyarsa, wawa ne, amma wanda yake tafiya cikin hikima zai kubuta. Wanda yake bayarwa ga matalauta, ba zai talauce ba, amma wanda bai kula da su ba, mutane da yawa za su la’ance shi. Mutane sukan buya sa’ar da mugaye suka samu iko, amma sa’ar da iko ya fita daga hannunsu adalai sukan karu.

Wanda ake ta tsawatawa a kai a kai, amma ya taurare, ba makawa tasa ta kare farat daya. Sa’ar da masu adalci suke mulki, jama’a sukan yi murna, amma sa’ar da mugaye suke mulki, jama’a sukan yi nishi. Wanda yake kaunar hikima yana faranta zuciyar mahaifinsa. Amma wanda yake abuta da karuwai zai lalatar da dukiyarsa. Sarkin da yake aikata adalci kasarsa za ta yi karko, amma wanda yake karbar rashawa zai lalatar da kasar. Mutum wanda yake yi wa makwabcinsa dadin baki yana kafa wa kansa tarko. Laifin mugun zai zama tarko a gare shi, amma adali zai rera waka, ya yi farin ciki. Adali yana sane da hakkin matalauta, amma mugun bai san wannan ba.Ashararai sukan sa wa birni wuta, amma masu hikima sukan kwantar da hasala. Idan gardama ta shiga tsakanin mai hikima da wawa, sai wawa ya yi ta fushi, ko kuwa ya yi ta dariya, gardamar dai ba za ta kare ba. Mutane masu kisan kai suna kin amintaccen mutum, amma adalai za su kiyaye ransa. Wawa yakan nuna fushinsa koyaushe, amma mutum mai hikima yakan kanne fushinsa. Idan mai mulki yana kasa kunne ga maganganun karya, dukan ma’aikatansa za su zama makaryata. Matalauci da azzalumi suna tarayya a abu daya, wato dukansu Ubangiji ne Yake ba su ganin gari. Idan sarki yana yi wa talakawa shari’ar gaskiya, zai dade yana mulki. Horo da tsawatarwa suna ba da hikima, amma yaron da aka sangarta zai jawo wa mahaifiyarsa kunya. Sa’ar da mugaye suke mulki, laifuffuka sukan karu, amma adalai za su ga faduwar wadannan mutane. Ka hori danka zai dadada maka rai, ya kuma faranta maka zuciya. In da ba a bin fadar Allah, jama’a za su kangare, amma mai farin ciki ne wanda yake kiyaye dokar Allah. Bara ba ya horuwa ta wurin magana kawai, gama ko da ya fahimta ma, ba zai kula ba. Ka ga mutum mai garajen yin magana? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi. Baran da aka shagwaba tun yana yaro, a karshe zai dauki kansa tankar magajin gida. Mutum mai saurin fushi yakan ta da fada, mai zafin rai kuma yakan aikata laifi da yawa. Girman kan mutum zai jawo masa kaskanci, amma za a girmama mai tawali’u. Abokin barawo mugun makiyin kansa ne, yana jinsa yana ta rantsuwa, amma ba zai ce komai ba. Jin tsoron mutane tarko ne, amma wanda ya dogara ga Ubangiji za a daukaka shi. Mutane da yawa sukan nemi farin jini daga wurin mai mulki, amma Ubangiji ne Yake yi wa mutum adalci. Mutum marar gaskiya abin kyama ne ga adali, adali kuma abin kyama ne ga mugun.

(Karin Magana 28, 29).