✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zakarar tseren mita 100: ‘Yar Najeriya, Tobi Amusan, ta zubar da hawaye

Buhari ya taya Amusan murna.

’Yar tseren Najeriya, Amusan Tobi, ta zubar da hawaye bayan lashe zinare a gasar tseren mita 100 ta mata zalla.

Amusan ta zama zakarar duniya a gasar tseren mai hade da tsallen shinge a gasar da aka kammala jiya Lahadi a birnin Oregon na kasar Amurka.

Amusan ta kafa tarihin kasancewa wadda ta tsallake matakin wasan gab da na karshe a dakika 12 da digo 12 a zagayen farko kana dakika 12 da digo 6 a zagaye na 2 yayin wasanta a filin Hayward.

Ta sha gaban ‘yar Jamaica Britany Anderson da ta zo ta biyu bayan kare nata gudun a dakika 12 da digo 23 kana Jasmine Camacho-Quinn ta Puerto Rico a matsayin ta 3.

Sai dai mahukuntan gasar sun ce baza a sanya nasarar ta Amusan a jerin wadanda suka kafa tarihin Duniya ba, la’akari da yadda aka samu nasarar gudun mita 2 da rabi a dakika guda.

Amusan ‘yar Najeriya ta yi nasarar karbe kambun ne daga hannun Keni Harrison ‘yar Amurka da ke rike da shi tun shekarar 2016.

A jawabinta bayan nasara a tseren, Amusan ta ce ko shakka babu ta yarda da kanta amma ba ta yi tsammanin zama zakarar Duniya nan kusa ba.

Buhari ya taya Amusan murna

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Amusan murnar daga martabar Najeriya a idon duniya.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Buhari ya ce ya shiga sahun miliyoyin ‘yan Najeriya wajen taya Tobi Amusan murna da bajintar da ta yi, a gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta 2022.

“Wannan sabon tarihi da Amusan Tobi ta kafa na samun lambar zinare, abin farin ciki da alfahari ne a wurinmu.

“A yanzu wannan daukaka da martaba da kasar nan ta samu silar Amusan zai sa taken Najeriya ya ci gaba da amo ko’ina a fadin duniya.”