✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asarar alli azargagiyar afatati

Aringizo Buri’u masu gizo Bobi ta dandani kudar gizo Yai mata kurege mai banzo Burgar Buzuzu bazo-bazo   Kowa ya zo Baba ne gwarzo Yai…

Aringizo

Buri’u masu gizo

Bobi ta dandani kudar gizo

Yai mata kurege mai banzo

Burgar Buzuzu bazo-bazo

 

Kowa ya zo

Baba ne gwarzo

Yai wa mazaje bozo

’Ya’ya a bara bwazo

Tunzurar miyagu ta furzo

 

Mun ga jagaliyar yawa

Jagoran jagaliyar Jijjiga-ciyawa

Sullutu mai sowa

Kyakkewar darawa

Dabarbarun dimuwa

 

Fuffukan fankan fayakau

Ga shi can sakayau

A tuntubi ganau da jiyau

Rayuwarsa bayau-bayau

Yana nan jiya i-yau

 

Tsohuwa na taba alli

Tai kadin zare sili-sili

Afatati mai hargitsa bulli

Azargagiya asarar alli

Jirkicewar rashin fasali

 

Bundunbalar kusu

Mugu mai yawan musu

Ka dai huda asusu

An mashe da kowa sususu

Tufkarka tai busu-busu

 

Wawurar waskon waku

Wulbitawar akwaku

Wuntsilagudi-gudin iya taku

Wautar  watangaririyar duku-duku

Waskiyar watsattsaken tsurku

 

Baragurbi dan gwanjo

Jigon jan ragamar ajo

Baban rawar banjo

Mai gayaunar Otawa Baba-Ojo

Burinsa gwabje su gwarjo

 

Murdiyar modi

Mai madi

Muba-mubin murde-murden murdi

Mai bikin gayyar sodi

Mai kantu soyayyen ridi

 

Rudun rubdugu

Rarewar kamun bugu

Burgar shan bugu

Ranar dama-damar dungu

Rangajin rawar burungu

 

Kalar Kadar kadi

Kada kuntukun kidi

Karime-karimen kanwar kudi

Karambanin kaudi

Katantawar karkarwar kodi

 

Hargowar hargitsi

Motsin matsi

Tsuwwa tsiyataku tsi-tsi

Yunburin yamutsi

An dai yi uwar-watsi

 

Zabarin zakwadi

Zumun zumudi

Sunkutar samarin sididin sodi

Turancin  taune-taunen  tandi

Botoromin baudi

 

Baba-Ojo mai gararumar garkar gayaunar Otawa ya yi saba da munanan zare, inda ya kai wa Baban-burin-huriyya rubdugun hare-hare, daidai sa’in da ake tunkarar zababbakar zabukan dubu baramin lauje da sili da manuniyar basa. Wannan dai ba wani sabon lamari ba ne, domin ya saba tsuwurwurta irin wannan kwakyariya, wadda a daidai wannan gaba aka hange ta tamfar ASARAR ALLI AZARGAGIYAR AFATATI.

Haurobiyawa, wai bushiya ce za ta yi wa kunkuru bafa, domin shi mai bahaya a dubara ba lallai ne ya nusar da wani muhimmancin tsarkake mabubbugar kashi da kafar tsula fitsari ba. Mai gararumar garkar gayaunar Otawa ya jefa azargagiyar zargi kan cewa Baban-burin-huriyya  na yunburin yi wa kansa aringizon buri’u, kuma shi mai KAMA-KARYA ne, kodayake dai bai dara Baba-Ojo a wajen KAMA-KARYA TAUNA CINYE KA HADIDIYE ba, wato lamarin ya yi ta tsuwurwurtawa a tsawon wa’adin mulkin mulaka’u na jam’iyya mai danboto da sanda jirge. Al’umma na sane da tabargazar GWANJON DAKAN-DAKA, SHIBAR-DAKA, TANKADEN BAKIN GADO, shirin da ya bai wa Baba-Ojo damar dama-damar damalmala dukiya da danniya. Shi kuwa Banen Baba-Ojo ya duma wasoso a kadarorin basar nan, har ya samu ya yi na kansa; kodayake dai wasu na wassafa cewa a zamanin da yake bwadago a hukumar tabaita fasa-bwauri ya dan dumbuzo badago, ya bar talakawa suna da kwado da jibon mandabo a dan bobo, har da masu mabobo.

A tattara tsintsiyar kwakwa da ’yar laushi a yi ta shara. Kuma a daukacin batutuwan ingarman barfe barafan tititin tarragon layin dogo, ba tare da bata lokacin wulwulawar hannayen agogo ba, na yi alwashin aron bakinku in ci muku albasa mai lawashi, a rage fushi, domin fafutika ce babu fashi. Fatanmu dai ka da jikin kowa ya yi yaushi, sai ma dai tumbi ya dauka tuntum da zarar kowa ya boshi.

’Yan jagaliya na kai naushi da gudumar kaushi, ga bakinsu na ta bashi-bashi, suna ta furta batutuwa da jifar mashi, wai su ga fitattun ’yan fashi. Sannanen lamari ne dai KWASHI-KWARAF da yi wa lalitar basa BARBAF, inda aka wawushe komai KAKAF, masu fashi da mubami ne suka tsuwurwurtata son ransu a zamanin jan ragamar mai danboto da sanda jirge. An dai dauki tsawon lokaci ana ta jirga al’umma.

’Yan makaranta, a yi hattara ka da TSOHON TSULA ya sha al’umma da BASILLA ga BANZAR BAZARA. Ba boyayyen batu ba ne in an yi la’akari da  dimbin damin dukiyar da Baba-Ojo da banensa suka wawure, tun farko dawowar tafarkin DAMON-KURAR-DIYYA, al’amarin da ya ba su damar juya akalar dama-damar wasan Samson-siya-siya da gwara burungun talakawa su yi ta sa-in-sa, yayin da su kuwa suka yi ta handame:

GURASA

GAMI DA MASA

GA WASA-WASA

ZUBE A KWANON TASA

SUKAI TA TAFKA TA’ASA

SUKA HANA ’YAN BASA SU KWASA

Kai su Baba-Ojo an WARWASA

To JIKI DAI MAGAYI BANKAR BUBIN DAN KORAU. Duk wanda ya zabo wa al’umma baragurbi, tabbas ya budo tabargaza babi-babi. Haurobiyawa da muguwar rawa gwamma bin tashi. Mai-duka dai Ya raba mu da ’yan fashi, su kuwa sai sun ci karo da karnai masu haushi.

Lallai mu yi karatun ta-natsu, mu bugi aura mu byale taiki, don gudun kada ai mana tutsu. Haurobiyawa kowa ya natsu babu mutsu-mutsu, kyawawan ayyuka muke hanboron ganin sun baibaye basa, sun warwatsu.