✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asusun ITF ya horar da matasa 300 sana’o i a Bauchi

Asusun haror da ma’aikata na kasa [ITF] ya horar da matasa 300 akan sana’o’i daban daban a jihar Bauchi don dogaro da kai. Darakta Janar…

Asusun haror da ma’aikata na kasa [ITF] ya horar da matasa 300 akan sana’o’i daban daban a jihar Bauchi don dogaro da kai.

Darakta Janar na ITF Joseph N. Ari, ne ya sanar da hakan yau Litinin a lokacin da ake tantance wadanda za a horar a cibiyar ma’aikatar kwadago da ke jihar Bauchi.

Joseph, ya ce horar da matasan sana’o’i na cikin shirin samar da ayyuka yi ga matasa da Shugaba Muhammadu Buhari, ke yi.

Manajan asusun ITF na reshen jihar Bauchi Richard A. Baba, ne ya wakilci Darakta Janar na asusun ITF, shirin an kaddamar da shi ne hukumar koyar da sana’o’I, wannan horarwa zai taimaka matuka wajen dakile kalubalen tattalin arzikin kasa.

An dai gudanar da horarwar a yankunan Azare da Misau da Bauchi da kuma Ningi.