✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Auratayya tsakanin Ibo da Hausawa ta kyautata zamantakewa a Kudancin Najeriya – Malamin Tarihi

Dokta Lawal Yusuf Fagge, masanin tarihi ne da ya shafe shekaru 23 yana koyarwa a Kwalejin Ilmi ta Tarayya (Alban Ikoku Federal College of Education)…

Dokta Lawal Yusuf Fagge, masanin tarihi ne da ya shafe shekaru 23 yana koyarwa a Kwalejin Ilmi ta Tarayya (Alban Ikoku Federal College of Education) da ke garin Owerri, Jihar Imo. A  hirarsa da wakilinmu, ya yi bayanin dalilin zuwan Hausawa da dadewarsu da zamantakewarsu da mutanen gari, wacce ta kai ga sarakunan Hausawa har suna auren mata kabilun Ibo domin kyautata zamantakewar.

A matsayinka na masanin tarihi, wane bayani za ka yi a kan dalilin zuwan Hausawa da dadewarsu a wannan sashe?
Tarihin zuwan Hausawa wannan sashe kashi uku ne. Na farko, akwai wadanda suka fara shigowa kafin zuwan Turawan da suka zo neman abubuwa kamar hauren giwa da karo da suke fataucinsu a tsakanin garuruwa na ciki da wajen Najeriya. Na biyu, akwai wadanda suka zo bayan Turawa sun ci Arewacin Najeriya a 1903 da suka mayar da garin Lakwaja ya zama hedkwatarsu, da suke tsare sarakunan Arewa da suka ki ba su hadin kai.
Sarkin Kano Alu Babba da Sarkin Katsina Abubakar da Sarkin Zazzau Kwasau da Sarkin Bidda Ibrahim, dukkansu Turawa ne suka tsare su a nan garin Lakwaja. Iyalai da bayi da masoyan wadannan sarakuna sun biyo su zuwa Lakwaja, domin girmama su da suka mayar da garin ya zama cibiyar kasuwancinsu. A cikinsu ne aka samu wadanda suka fara tunanin yin tafiya zuwa gaban Lakwaja da suka isa garin Anaca a cikin 1907. Na uku, su ne Hausawan da suka shigo wannan sashe bayan Najeriya ta samu ’yanci a 1960.
Bayan sun isa garin Anaca, sun ci gaba da zaman dindindin a garin ne, ko me suka rika yi? Ba su yi zaman dirshan a wancan lokaci ba, suna zuwa ne a matsayin ’yan cirani da suke sayar da kayan adire da sakakkun tufafi na Nupe da makamantansu ga kabilun Ibo, bayan shekara daya ko biyu su koma.
Daga 1907 ne Hausawa suka fara zaman dindindin a wannan sashe da aka samu Sarkin Hausawa Yahya a Owerri da Sarki Haruna a Enugu da Sarki Usman a Umma Ahiya da Sarki Bako na Elele, wato mahaifin tsohon Gwamnan soja na Jihar Akwa Ibom Kanar Yakubu Bako.
Ko akwai Hausawa ’yan shekaru 70 zuwa 80 da aka haife su a wannan sashe?
kwarai kuwa, kamar Sarkin Hausawan Owerri, Alhaji Baba Sule. An haife shi a 1937, yanzu yana da shekaru 78. Akwai yayyensa da aka haife su a wannan sashe a tsakanin 1914 zuwa 1927 da suka riga mu gidan gaskiya.
Yaya zamantakewar Hausawa baki da kabilun Ibo ’yan gari?
Wannan sai godiya ga Allah, domin muna zaune lafiya. Hakan ne ya haifar da kyakkyawar dangantaka, wanda yanzu haka mafi yawancin sarakunan Hausawa da ke mulki a garuruwa daban-daban na sashen kudu maso gabas suna auren mata kabilun Ibo da suke zaune tare. Masu auren mata 2 zuwa 4 za ka same su sun yi raba daidai ne wato, biyu kabilun Ibo da sauran mata 2 Hausawa. Ta fannin kasuwanci, akwai cudanyar da ta haifar da amincewarsu da suke ba mu kaya muna sayarwa, mu debe ribarmu mu mika masu uwar kudi su ma suna karba daga gare mu.
Amincewa da suka yi da mu, ya sa akwai da yawa daga cikin kabilun Ibo da suke mika wa Hausawa kudade masu yawa domin gudanar da harkokin kasuwanci; wanda ba zai iya bayar da irin wannan kudi ga dan uwansa ba.
Wannan ya nuna ke nan babu matsalar samun guraben ayyuka ga ’ya’yanku daga gwamnatocin jiha da kananan hukumomi a wannan sashe?
Daga bangaren Gwamnatin Tarayya babu laifi, ana samun guraben ayyuka domin muna zaune tare da su lafiya. Babu wani bambanci a tsakaninmu da su a kan abubuwan da suka shafi kasuwanci.
Yaya batun kabilanci da ikirarin da kabilun Ibo suke yi na kafa kasar Biyafara. Ba ka ganin hakan yana iya jefa ku cikin halin fargaba?
Tun bayan yakin basasa muke zaune lafiya da kabilun Ibo a wannan sashe. Idan mutane masu ikirarin kafa kasar Biyafara suna gudanar da abubuwansu, ba su taba wani dan Arewa; suna rigima ne da mahukunta na kasa baki daya. Dukkan mutanenmu ’yan Arewa da suka hada da leburori ’yan cirani da masu tallar kaya a kan hanya da ’yan kasuwar dabbobi da masu shaguna da rumfuna a kasuwanni suna gudanar da harkokinsu lami lafiya ba tare da tsangwama ba.
Kuma ba a taba samun labarin sun auka wa mutanenmu da duka ko kwace kayansu a kan hanyoyi ba. Kuma tun da aka samu canjin gwamnati sai aka samu saukin kalaman batanci da wasu suke yi wa Hausawa.
Wane kira za ka yi wa ’yan Arewa da ke zaune a wannan sashe?
A matsayin malamin Jami’a, ina yin kira ga dukkan ’yan Arewa da mu kasance jakadun kirki, mu rike gaskiya da girmama dokokin wuraren da muke zaune. Idan wani abu ya taso, mu hanzarta sanar da mahukunta, mu daina bari ana samun baraka daga gare mu. Kuma mu yi kyakkyawar lura da irin mutanenmu da suke zuwa cirani a garuruwan da muke zaune a wannan sashe na Najeriya.