✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Auren Dole: kalubale ga ’ya’ya mata

Salamu Alaikum. Da farko dai ina son ne jama’a su dan ara min hankali da tunaninsu. Domin yin hakan zai sanya su fahimce ni kuma…

Salamu Alaikum. Da farko dai ina son ne jama’a su dan ara min hankali da tunaninsu. Domin yin hakan zai sanya su fahimce ni kuma su amfanu da abin da nake son na yi bayani a kansa.
Na farko dai, a duk lokacin da aka yi magana a kan auren dole, to kai tsaye sai a dora alhakin al’amarin kacokan a kan iyaye. To, abin da nake tambaya a kansa a nan, shin mahaifa ba su da alhaki na zabarwa ’yarsu mijin da za ta aura ne? Kuma shin su ’yan matan ba su da laifi ne? To, mai karatu bari har gaba, wato, ba yanzu nake son ka ba ni amsar wadannan tambayoyin ba.
Idan aka ce auren dole za a iya cewa yi wa yarinya aure da wanda ba ta so, ko kuma yi wa namiji aure da wacce ba ya so. Wanda idan hakan ta faru, to, mafi akasari mata ne suka fi shiga cikin matsalolin rayuwa, inda wasu suke guduwa su shiga uwa duniya, wasu kuma su kekashe kasa su ki zama da mijin a karshe dai har a raba ta da mijin. Wani lokacin kuma wata tun farko ba za ta bari a yi auren ba domin a karshe za ta sami rinjaye ga iyayenta har su fasa yi mata auren. To, a nan waye ake gani da laifi, shin yarinyar ko kuma mahifanta?
Wasu suna dora alhakin duk wani abu wanda ya faru a wannan bagire a kan mahaifan yarinya su kadai. Wanda a gaskiya kuwa idan aka aikata haka, to, ba a yi adalci ba. Shin tun farko waye shari’a ta dora wa alhakin aurar da ’ya mace. Shin mace aka yarda ta aurar da kanta, ko kuma iyaye ne suke da alhakin aurar da ’yarsu?
A shari’a dai yadda aka bayyana shi ne, mahaifi ne yake da alhakin aurar da ’yarsa kuma shi yake da alhakin lura da mijin da ’yarsa ta jajibo masa, idan na kirki ne ko akasin hakan. A nan ke nan babu inda shari’a ta hana mahaifa su aurar da ’yarsu a kan wanda yake mutum ne na kirki kuma babu inda aka hana su da su hana ’yarsu ga wanda ba na kirki ba, ko wanda ba ya da addini.
Idan har ya kasance hakan, to ta wace hujja ko kuma meye dalilinki a kan cewa wai wanda rayuwarki take so shi za ki aura koda kuwa ba na kirki ba ne? Koda ba ya da addini, koda ba ya da asali ko tsatso na mai tsarki. An gaya wa mahaifanki kuma sun yi bincike sun tabbatar da cewar ba mutumin kirki ba ne. Kuma sun gaya maki amma sai kika ce ke kin ji kin gani shi kike so, ko kuma shi za ki aura.
Kuma idan za a yi auren, mahaifanki ne kike son su saya maki kayan daki. Su kike so da su gayyaci mutane na nesa da na kusa kuma su yi maki abubuwa na kece raini a kan ganin an yi buki na fitar-raini. Amma kuma wai duk da wanda kika zabar wa kanki ba wanda suke so ba.
Ki tuna fa bayan kokarin da mahaifinki ya yi wajen hada kudin da ya auro mahaifiyarki, haka ya yi fadi-tashin ganin ya samu abin da za su ci, shi da ita. Suna bisa wannan siradi na rayuwa har Allah Ya bayar da cikinki, suka yi renon cikin shi da mahaifiyarki har aka haife ki, kika zo duniya. Suka ciyar da ke, suka tufatar da ke, suka shayar da ke. Suka sanya ki makaranta, su ka kula da ke a lokacin da ba ki da lafiya, suka kula da ke wajen ganin sun biya maki bukatun rayuwarki. Ki tuna fa duk wannan lokacin ba su da yakini a kan cewa za ki rayu ko kuma za ki zama wata abu a duniya. A’a, duk sun yi kasada ne.
Kuma zan iya fada maki cewa, cikin wancan lokacin akwai lokacin da kilan a kan kudin makarantarki, ko a kan tufafin sallarki, ko kuma a kan maganin rashin lafiyarki akwai lokacin da wani ya gaya mahaifinki bakar magana, akwai lokacin da ya zo wajen wani neman taimakonsa ya hana masa, karshe har ya yi masa korar kare, amma duk haka zai hakura ya koma wajen wani. Shi dai bukatarsa kawai ya ga ya kauda taki matsalar.
Kuma idan kin shiga wata matsala, kilan kin hadu da wata rashin lafiya mai kazanta wacce ake gudun wanda yake da ita. Mamarki da babanki ba za su guje ki ba, a’a, za su ma zama wadanda za a rika kyama da gudu a kan zamansu dake.
Kawai laifi daya ne za a iya a dora wa iyaye, shi ne nisantar ’ya’yan da mahaifa suke yi a wannan zamani. A nan ina nufin yadda al’adar Bahaushe ta koma yanzu. Za ka ga mahaifi bai cika dariya ko wasa da ’ya’yansa ba, ko kuma da wuya ka ga mahaifin da yake zaunawa da ’yarsa yake tattaunawa da ita a kan matsalolin rayuwa. Shi a daukarsa idan hakan ta faru wai za a raina shi, wani ko matarsa ba ya sakar wa fuska, a’a, dariyarsa a wajen gida take, a majalisa ko a kasuwa da sauran wuraren da yake hira. Amma da malam ya dawo gida idan yunwa ta koro shi ko wata lalura to, zai shigo gida a gimtse, wani tun a zauren gida zai tsaya ya canza fuska wai kada ya yi dariya matarsa da ’ya’yansa su raina shi.
Haka mahaifiya mace, da yawa za ka ga tsakaninsu ita da ’yarta daga tsawa sai hantara, wata ma har da zagi ko duka take yi wa ’yarta. Amma babu ranar da za ta zauna da ita suna labarin duniya da tattaunawa a kan matsalolin rayuwa. To, idan hakan ta faru sai yarinya ta ce ga wanda take so, mahaifi ya ce a’a shi ga wanda zai hada ta da shi. Kuma zai kira ta cikin tsawa ya gaya mata cikin gadara da nuna isa wai shi a dole mahaifi, zai shaida ma ta cewar, wai ba zai bai wa wane aurenta ba, a’a, da wane zai hada ta. Ko kuma ya gaya wa mahaifiya cewa ta gaya wa ’yarta ya hada ta da wane. Kuma a nan ko mahaifiyar idan tana son ta ganar da shi wani abu a kan halin da ’yarsa take ciki to, ita ma tsawa zai yi mata ba ma zai saurari bayyaninta ba.
Za mu ci gaba