✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban Hafsan Tsaro ya ce kalubalen tsaron Najeriya ya kusa kawo karshe

Babban Hafsan Tsaro, Janar Aboyomi Gabriel Olonisakin ya ce kalubalen tsaro da Najeriya ke ciki ya kusa kawo karshe. Janar Abayomi ya bayyana haka ne…

Babban Hafsan Tsaro, Janar Aboyomi Gabriel Olonisakin ya ce kalubalen tsaro da Najeriya ke ciki ya kusa kawo karshe.

Janar Abayomi ya bayyana haka ne a wajen bikin yaye kuratan sojoji karo na 78 da ya gudana a Barikin Daffo da ke Zariya a karshen makon jiya.

Janar Olonisakin ya ce kalubalen tsaron da ya hada da satar mutane don neman kudin fansa da kisan mutane ba tare da sun aikata wani laifi ba da Boko Haram da fashi da makami da ayyukan matsafa duk za su zamo tarihi a Najeriya.

Ya ce tsarin fadakarwa da wayar da kan jama’a kan ababen masu fashewa da ake yi ga jama’a ya yi matukar tasiri, kuma horar da kuratan sojoji a kansa da illolinsa zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu na soja a duk inda suka tsinci kansu.

Saboda haka sai ya bukaci sababbin sojojin su kasance masu sadaukar da kai a lokacin da suke gudanar da aikinsu ga kasa.

Ya kuma tunatar da sojojin rantsuwar da suka yi na kasancewa masu biyayya da aiki bisa umarni, wanda a cewarssa wannan ne ya sanya suka kasance masu matsayi na musamman bayan da suka kammala rantsuwa.

Haka kuma ya shawarce su da su kiyaye shiga ko aikata duk wani abin da zai bata sunan sojojin Najeriya da kuma kimarsu tare da mutuncin Najeriya a yayin gudanar da ayyukansu.

Janar Olonisakin ya yaba da kwazo da juriyar da jami’an da suka horar da sojojin a karkashin Kwamandan Makarantar, Manjo Janar Sani Muhammad tare da yin alkawarin ci gaba da bai wa makarantar horar da kananan sojojin gudunmawar da ya kamata.