✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban Sufeton ’Yan sanda ya ziyarci Katsina

Babban Sufeton ’Yan sandan kasa Solomon Arase ya kai ziyara don  tattaunawar keke da keke da kungiyoyi da masu ruwa da tsaki da sauran al’ummar…

Babban Sufeton ’Yan sandan kasa Solomon Arase ya kai ziyara don  tattaunawar keke da keke da kungiyoyi da masu ruwa da tsaki da sauran al’ummar Jihar Katsina a shekaranjiya Laraba.
Taron wanda aka yi a dakin taro na Ma’aikatar  kananan Hukumomi ta Jihar Katsina, Babban Sufeto ya shaida wa mahalarta taron cewa, ya zo jihar ce domin su tattauna a kan abubuwan da suka shafi tsaro ba a jihar  kadai ba har da kasa baki daya.
Mista Salomon Arase ya ce, kofarsa da kuma ta hedkwatar ’yan sandan kasar nan tun daga kananan hukumomi har zuwa matakin kasa a bude take domin karbar shawarwari ko wani rahoto da zai taimaka wajen samun ingantaccen tsaro a kasar nan.
Ziyarar aikin ta yini daya da Babban Sufeton ya kai na da nufin kara dankon zumunci tare da fahimtar juna a tsakanin jami’an ’yan sanda da sauran jama’a da kuma sauran takwarorinsu na tsaro.
Tun farko sai da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Katsina Usman A. Abdullahi ya shaida wa masu ruwa da tsakani a wajen taron cewa, Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da ake fama da matsalolin barayin shanu da yanzu  za a iya cewa ya fara zama tarihi. Sai dai ya yi gargadi ga wuraren da ke tara jama’a irin su otal-otal da tashoshin mota da sauransu su kara sa ido a kan irin mutanen da suke mu’amulla da su.
daya daga cikin mahalarta taron Alhaji Muhammadu Usman Sarki ya ce tun kafuwar Jihar Katsina ba a taba samun irin wannan ganawa ba a tsakanin jama’a da hukumomin ’yan sanda don tattaunawa a kan abin da ya shafi tsaro.  A kan haka ne ya jinjina wa Babban Sufeton da kuma Kwamishinan ’Yan sanda na jihar a kokarin da suka yi na hada wannan taro.
Mahalarta taron dai sun hada da kungiyoyin ’yan banga da na direbobi, wato NARTO da NURTW da wakillan masarautun Katsina da Daura da sauran masu ruwa da tsaki a  harkar tsaro da ke fadin jihar.