✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban taro: Hukuncin kotu ya jefa PDP cikin halin rashin tabbas

A ranar Juma’ar ne dai ake sa ran kotun za ta yanke hukunci a kan taron.

Wata kotun daukaka kara da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas ta jinkirta yanke hukunci a kan karar da tsohon Shugaban PDP na kasa, Uche Secondus ya shigar da jam’iyyar kan babban taronta, har zuwa ranar Juma’a.

Jam’iyyar dai ta shirya gudanar da babban taron nata ne ranar 31 ga watan Oktoban 2021, sai dai hukuncin kotun na iya shafar yiwuwar yin taron a ranar.

Yanzu haka dai ana zaman dar-dar a jam’iyyar, kasancewar ba a san me shari’ar za ta haifa ba.

Tun da farko dai kotun ta sanya Alhamis a matsayin ranar da za ta yanke kwarya-kwaryar hukunci a karar da Secondus ya maka PDP a gabanta, yana neman a dakatar da taron, sannan ta ba shi damar shirya shi da kansa a nan gaba.

Sai dai lokacin da kotun ta fara sauraron karar a ranar Talata, sai wasu mambobin jam’iyyar su shida suka nemi a saka su a cikin masu korafi, amma lauyan Secondus din ya ki amincewa.

Amma alkalan kotun sun amince da bukatar masu neman shiga shari’ar.

Alkalin da ya jagoranci zaman kotun, Mai Shari’a Haruna Simon Isammani, bayan sauraron muhawarar bangarorin karar biyu, ya umarci lauyan mai kara da ya ba wanda ake karar kwafin tuhume-tuhumen cikin awa 24, inda shi ma ta ba shi awa 24 don ya kare kansa.

Akalin dai ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 28 ga watan Oktoba, yayin da ya sa ranar Juma’a a matsayin ranar sauraro da yanke hukunci kan bukatar ta Secondus.