✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban Taron APC: Abin da ya sa Kwamitin Buni ke jan kafa

Wasu majiyoyi sun ce Gwamna Buni na so ne ya cimma wani buri.

Sababbin bayanai sun fayyace abin da ya sa Kwamitin Riko na APC a karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni yake ta shiriritar da shirin Babban Taron jam’iyyar na kasa.

Wasu manyan jam’iyyar sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa da gangan Kwamitin na Buni yake jinkirta gudanar da taron da nufin cimma wata manufa tashi ta siyasa da ta wasu tsirarun mutane.

Daya daga cikin majiyoyin, wani tsohon Gwamna, ya ce ana ta shiriritar da lamarin ne saboda Gwamna Buni yana da burin zama Shugaban Kasa.

“Wannan ba komai ba ne illa [kare wani] muradi na kashin kai. So yake ya zama Shugaban Kasa ko ana ha-maza-ha-mata, ko kuma, idan hakan ya ci tura, Mataimakin Shugaban Kasa”, inji tsohon Gwamnan.

Wani tsohon Gwamnan kuma cewa ya yi Kwamitin na jan kafa ne don ya samu damar gudanar da Babban Taron da zaben fid da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a lokaci guda.

Ba zabi

Tsohon Gwamnan, wanda kuma da shi aka kafa jam’iyyar, ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta daukar mataki domin ceto jam’iyyar.

A cewarsa, “Idan Shugaban Kasa ya sa hannu a kan sabuwar dokar zabe, to za a yi zaben fid da gwani a tsakanin watan Yuni da watan Yuli ke nan.

“Ka kuwa san cewa dokar ta tanadi cewa a yi zaben fid da gwani wata shida kafin babban zabe.

“Abin da muke gani shi ne jam’iyyar za ta shiga rudani saboda suna so su yi Babban Taron da zaben fid da gwani a lokaci guda domin masu korafi game da abin da zai biyo baya su kasance ba su da wani zabi”, inji shi.

Babban rudani

Ranar Litinin jam’iyyar ta afka cikin rudani bayan dage Babban Taron har sai abin da halin ya yi.

A da dai an shirya gudanar da taron ne ranar 26 ga watan Fabrairu.

Can da tsakar rana kuma Kwamitin, ta hanyar wata takarda da ya aike wa Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ya ayyana ranar 26 ga watan Maris a matsayin ranar gudanar da manyan tarurrukan jam’iyyar na shiyya.

Amma fa takardar, wadda Gwamna Buni da Sakataren Kwamitin, Sanata    Senator John James Akpanudoedehe, suka sanaya wa hannu, ba ta ce uffan ba game da ranar yin Babban Taron na kasa.

Sai dai kuma bayan wannan labarin ya kai kunnuwan kusoshin jam’iyyar, Kwamitin ya sha matsin lamba a kan ya sake shawara.

Wasu majiyoyi sun ce wani bangare na Fadar Shugaban Kasa da wasu Gwamnoni da ma wasu masu sha’awar darewa kujerar shugabancin jam’iyyar sun soki wannan shawara ta Kwamitin.

Wannan ne ya sa da misalin karfe 7:00 na dare Kwamitin ya lashe amansa, ya ayyana 26 ga watan Maris a matsayin ranar Babban Taron bayan wata doguwar tattaunawa.

Da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatar jam’iyyar, bayan wata ganawar sirri ta sa’o’i da dama, Sakataren Kwamitin, Sanata Akpanudoedehe, ya ce ranar 24 ga watan Fabrairun 2022 za a fara shirye-shiryen taron.

A cewarsa, gabanin Babban Taron na kasa za a gudanar da manyan tarurrukan shiyya.

“Bayan an tattauna an cimma yarjejeniya da Kwamiti, mun amince a fara shirye-shiryen gudanar da Babban Taron jam’iyya daga 24 ga watan Fabrairu a kuma kammala ranar 26 ga watan Maris

“Ma’ana shirye-shiryen Babban Taron za su kankama ranar 24 ga watan Fabrairu a kuma karkare komai ranar 24 ga watan Maris a dandalin Eagle Square,” inji shi.

Mudashir da Saawua Terzungwe da Muideen Olaniyi suka rubuta wannan rahoton.