✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban taron jam’iyyar PDP zai iya tarwatsa jam”iyyar- Adeniran

Shugabannin jam’iyyar PDP sun ce babban zaben da jam’iyyar za ta yi na fidda gwani zai nuna irin sa’ar da jam’iyyar take da shi a…

Shugabannin jam’iyyar PDP sun ce babban zaben da jam’iyyar za ta yi na fidda gwani zai nuna irin sa’ar da jam’iyyar take da shi a zaben shekarar 2019 tare da nuna yadda masu zabe za su dauki jam’iyyar.
Tsohon Ministan Ilimi kuma Tsohon Jakadan Najeriya a Kasar Jamus, Farfesa Tunde Adeniran da Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ibrahim Mantu sun ce taron da jam’iyyar za ta yi a ranar tara ga watan Satumba zai nuna makomar jam’iyya a babban zaben da za a yi a kasar a shekarar 2019.
Da yake bayyana wa duniya sha’awarsa na neman takarar shugaban jam’iyyar a taron da jam’iyyar ta gudanar a Abuja, Farfesa Adeniran ya ce zaben gaskiya ne kawai zai bayar da tabbacin dorewar jam’iyyar a shekaru masu zuwa.