✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babbar Kotun Jigawa ta kori karar karar da aka kai Saminu Turaki

Babbar Kotun Jihar Jigawa ta 4 da ke Dutse ta kori karar da gwamnatin jihar ta shigar tana tuhumar tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Saminu…

Babbar Kotun Jihar Jigawa ta 4 da ke Dutse ta kori karar da gwamnatin jihar ta shigar tana tuhumar tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Saminu Turaki da wasu mutum uku bisa zargin karbar Naira biliyan hudu daga bankin Guaranty da sunan za a yi aikin wasu hanyoyi a jihar amma ba a yi ba. Gwamnatin ta yi zargin cewa an yi amfani da sunan wani kamfani mai suna Gathel Nigeria Limited, mallakar dan uwan tsohon Gwamnan ne wajen karkatar da kudin. Alkalin kotun Mai shari’a Ubale Taura ya ce saboda rashin shaidu masu gamsarwa kuma gwamnatin jihar ta gaza wajan bayar da kwararan dalilai kan zargin ya sa kotun ta kori karar. Mai shari’a Taura ya kara da cewa karar ba a shigar da ita bisa ka’ida ba, saboda wadannan dalilai ne kotun ta kori karar.