✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Babu ruwan Grace a shiriricewar Mugabe – ‘Yar Majalisa

Wata ‘yar majalisar dokoki a jam’iyyar adawa ta Zimbabwe, Priscilla Mushonga ta ce rashin adalci ne a dora wa Grace Mugabe laifi kan kwaranyewar farin…

Wata ‘yar majalisar dokoki a jam’iyyar adawa ta Zimbabwe, Priscilla Mushonga ta ce rashin adalci ne a dora wa Grace Mugabe laifi kan kwaranyewar farin jinin mai gidanta.

BBC ta ruwaito Priscilla Mushonga tana cewa: “Ina jin abu ne mai sauki a zargi mace da laifi. Duk da yake, Shugaba Mugabe ya fara shiriricewa ne tun cikin 1983 lokacin da ya kashe mutum dubu 20 a yankin Matabeleland. 

“Mai yiwuwa a lokacin Grace tana aji daya ne a sakandare.”

Priscilla Mushonga ta ce eh, tana iya kasancewa a tsakiyar harkokin mulki yanzu amma ita kawai karan kada miya ce da Mugabe ke amfani da ita don ci gaba da mulki.

“Don haka a dora komai a kan Grace, ina jin irin abin nan ne na nuna son kan maza, kuma matukar raini ne ga jinsin mata.”

Ana kallon Grace Mugabe a matsayin wadda shugaban yake kokarin ganin ta gaje shi a kan gadon mulki, idan ya yi murabus.

Mista Mugabe dai ya kori mataimakinsa Emmerson Mnangagwa saboda zargin rashin biyayyarsa, abin da ya harzuka matakin da sojojin suka dauka, har ta kai ga saukar Robert Mugabe daga mulki.