✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bahaushiyar Saudiyya na yaki da wariyar launi

Wata ’yar asalin Hausawan kasar Saudiyya, mai suna Nawal Al-Hawsawi, matukiyar jirgin sama ta himmatu wajen fafutikar yaki da wariyar launin fata a kasarta ta…

Wata ’yar asalin Hausawan kasar Saudiyya, mai suna Nawal Al-Hawsawi, matukiyar jirgin sama ta himmatu wajen fafutikar yaki da wariyar launin fata a kasarta ta haihuwa.
Abin da ya faru kuwa shi ne, a ranar bikin kasa ta Saudiyya, sai Nawal ta shiga wani katafaren kantin sayar da kayayyaki a birnin Makka, don ta yi sayayya, sai kawai wata Balarabiya ta kirata da sunan baiwa, wato “Abda” a cikin harshen Larabci.
Matar da ta kira Al-Hawsawi da sunan kaskanci, ta yi nuni da cewa wata al’ada ce ta Larabawa da suke kiran bakaken fata don su muzanta su.
Nawal dai ta bayyana aniyarta ta rubuta littafi akan wariyar launin fata a kasarta ta haihuwa. “Manufata ba ta kururuwa ba ce a kan labarin abin da ya same ni. Wannan al’amari ne kana bin da ya shafe ni ni kadai ba, a’a, illa dai akwai ina da bukatar yin tsokaci kan nuna wariyar launi a cikin al’ummar mu,” injita.
A lokacin da takaddama ta kaure tsakanin Al-Hawsawi da Balarabiya, sai ta kirawo jami’in tsaron kanti da wani dan sanda, inda ta gabatar da korafinta kan yadda aka muzantata.
An gabatar da kara a wajen hukuma, inda a halin yanzu take gudanar da bincike. “Na dauki hayar lauyoyi biyu. Kuma ina da yakinin cewa za a tabbatar da adalci a shari’a, sannan a kawo sauyi. Bai kamata a yi watsi da wannan aibatawar ba, kuma ba za a amince da muzantawa karara ba,.” Inji Al-Hawsawi.
“A lokacin da aka yi zaman kotu, iyalan wannan mata da ta aibata ni sun roki afuwa, inda suka bukaci in janye karar. Na jajirce kan ci gaba da karata a kotu,” a cewarta. “Na tabbatar sun tafka kuskure duk da cewa su mutanen kirki ne, amma na yanke matsaya a kan wannan kara, wadda ba zan bayyanata ba, har sai littafina ya fito,” injita.
Al-Hawsawi ta yi karatun tukin jirgin sama a kasar Amurka, sannan ta samu shaidar kwarewar tukin jirgi a shekarar 2008.
Kuma ita mai fafutikar hakkin dan Adam ce, wadda ta himmatu wajen kyautata rayuwar al’umma a masarautar Saudiyya, musamman a kungiyarta mai lakabin “Adam” da ke da manufar yaki da wariyar launi a ofishinta da ke birnin Makkah.
A cewarta, manufar fafutikarta, ita ce, kawar da kowace irin nuna waroiyar launi ga mata da bakin ’yan kwadago da kabilanci a tsakanin al’ummomin Saudiyya.
“Sannan ina fata kawo sauyi a kafafen yada labaran kasashen Larabawa, wadanda ke bayar da muhimmanci kan nuna nakasun bakaken fata, inda suke nuna gazawa wajen fito da nasarorin da irin wadannan mutane suka samu a rayuwa,” injita.
A daidai lokacin da aka kammala tattara wannan rahoto, Nawal Al-Hawsawi ta janye kararta, amma za ta ci gaba da fafutikarta ta yaki da wariyar launi a kasar Saudiyya. Kuma littafinta mai taken “Abda” na nan fitowa.