✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Baki shi ke yanka wuya

Barkanmu da warhakaManyan Gobe Yaya hutu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon kawunku Naseeru Taneemu Annuree ya kawo muku labarin Baki Shi…

Barkanmu da warhaka
Manyan Gobe

Yaya hutu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon kawunku Naseeru Taneemu Annuree ya kawo muku labarin Baki Shi Ke Yanka Wuya. Ina fata za ku bi labarin sau-da-kafa don ci ribar darussan da yake koyarwa.
 
A sha karatu lafiya.

Taku: Amina Abdullahi

Baki shi ke yanka wuya

Daga Naseeru Taneemu Annuree

An yi wani lokaci da wadansu matasa biyu; Bakano da Bazazzage suke fada, hakan ya sanya mutane suka taru, domin raba fadan. Bayan an raba su sai Bakanon ya kama gabansa, yana fadin “Wallahi sai na yi maganinsa.”
To dama Bazazzage yana fama da ciwon ciki, inda a daren ranar ciwon ya sake taso masa har rai ya yi halinsa. Ko da gari ya waye mutane suka ji labarin ya mutu, sai suka fara zargin Bakanon saboda kalaman da ya yi cewa sai ya yi maganin Bazazzagen. Ba tare da bata lokaci ba ’yan sanda suka je suka tasa keyarsa bisa zargin kisan kai. Bakano ya yi magiyar duniyar nan kan ba shi ya kashe Bazazzage ba amma duk a banza. A karshe aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai.
Don haka ina fata Manyan Gobe za su kasance masu hakuri da kuma hadiye kalaman da idan sun furta su za su iya daure kansu.