✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun aure: Zan wahalar da maza – Tsohuwar matar Frank Edoho

Katherine Obiange, tsohuwar matar fitaccen dan fim din Najeriya, Frank Edoho, wanda kuma shi ne mai gabatar da shirin gasar MTN na ‘Who Wants To…

Kathering ObiangKatherine Obiange, tsohuwar matar fitaccen dan fim din Najeriya, Frank Edoho, wanda kuma shi ne mai gabatar da shirin gasar MTN na ‘Who Wants To Be A Millonaire,’ ta ce babu ita babu maganar aure a yanzu.
Kamar yadda ta fada a tattaunawarta da kafar watsa labarin fina-finan Najeriya ta intanet, Nigeriafilms.com, ta ce duk ma namijin da zai neme ta da wannan batu, to kamar bata lokacinsa zai yi, domin kuwa za ta wahalar da shi.
Katherine, wacce aurenta da Frank ya rabu shekaru uku da suka gabata, ta ce a halin da ake ciki, akwai zawarawa masu yawa da ke zawarcinta, sai dai duk da haka, ta sha alwashin cewa duk wanda ma ta amince wa zai wahala sosai, domin kuwa ba za ta amince su yi aure a yanzu ba.
Kamar yadda ta ce: “A yanzu kam ina cikin hutu, idan dai batun aure ne. Ina da kananan yara da ke neman kulawa ta. Haka kuma, ga wadda ta yi zaman aure na tsawon lokaci kama ta, abu ne mai kyau in saurara, in tunkari wani al’amari kuma na daban. A halin yanzu neman kudi nake yi, idan na tara su, zan ba ’ya’yana irin kulawar da ta kamace su. Don haka alkiblata ke nan a yanzu, amma ba batun aure ba.”
A lokacin da take kara tabbatar da matsayin da ta dauka game da batun na aure, ta kara da cewa: “Iyayena, musamman ma mahaifiyata ta tambaye ni game da batun sake aure. Ni kuwa ina cikin harkokina ne, wadanda suka hada da shirin fim din ‘Lekki Wibes Season II.’ Don haka duk namijin ma da ya kusance ni da batun aure zai wahala matuka, domin kuwa ban shirya ba.” Inji ta.