✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Belgium ta kwashe Kiristoci 250 daga Siriya

A shekaranjiya Laraba ne kasar Belgium ta fitar da wasu mutum 250 galibinsu Kiristoci ‘yan gudun hijirar kasar Siriya daga birnin Aleppo da yaki ya…

A shekaranjiya Laraba ne kasar Belgium ta fitar da wasu mutum 250 galibinsu Kiristoci ‘yan gudun hijirar kasar Siriya daga birnin Aleppo da yaki ya yi wa raga-raga a wani aikin sirri, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.

Wani kakakin gwamnati ya ce an gudanar da aikin ne a cikin wata biyu a wani amsa kiraye- kirayen taimakawa Kiristoci da sauran mutanen da suka makale a Aleppo tare da barazanar muzguna masu.
kungiyoyin masu fafutika ne suka fitar da ‘yan gudun hijirar wadanda suka hada da Yazidawa, ta budaddiyar hanya daya tal wacce ke kaiwa kan iyakar kasar Lebanon daga Aleppo.
Daga nan Ofishin Jakadancin Belgium a birnin Beirut ya gana da su sannan ya kai su Belgium a inda wasunsu ke da dangi, kuma za su iya neman mafaka.’Yan gudun hijirar kasar Siriya ne kadai suke samun irin wannan mafakar daga Belgium, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin kasar ta bayyana.
Tsawon shekara uku ke nan da yaki tsakanin ’yan tawaye da dakarun gwamnati ya daidaita birnin Aleppo. Kafin yakin, kasar Siriya ce ta fi yawan mabiya addinin Kirista a yankin Gabas-ta-Tsakiya, inda yawansu ya kai dubu 160.