✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Birtaniya na neman bahasin yadda Najeriya ta cafke Nnamdi Kanu

Birtaniya na neman bayani kan halaccin cafke Nnamdi Kanu.

Birtaniya ta ce tana neman bayani daga gwamnatin Najeriya game da cafke shugaban haramtacciyar kungiyar masu rajin kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu.

Jakadan Birtaniya a Najeriya ya shaida wa BBC cewar gwamnatin Birtaniya na neman bayani daga gwamnatin Najeriya a kan yiwuwar halaccin yadda aka kama Kanu.

  1. Tuwo ya yi ajalin mutum 9 ’yan gida daya a Zamfara
  2. Osinbajo zai halarci bikin mika sanda ga Sarkin Kano

Mai magana da yawun jakadan Birtaniya a Abuja, Dean Hurlock ya bayyana cewar ba a Birtaniya aka kama Kanu ba.

Ya ce Birtaniya za ta sanya ido tare bibiyar yadda shari’ar da za ta kaya.

Shugaban IPOB, mai shekaru 53 yana da katin shaidar zama dan kasa na Najeriya da kuma Birtaniya.

Ana tuhumar Kanu da yi wa mutane ingiza mai kantu ruwa, cin amanar kasa, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da sauransu.

Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Kasa Abubakar Malami SAN ne, ya bayyana wa manema labarai yadda aka cafke Kanu, a ranar Talata.

Tuni dai an gabatar da Kanu a gaban Mai Shari’a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ta bai wa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS umarnin tsare shi tare da neman a sake gabatar mata da shi a ranar 26 ga watan Yuli, 2021 don ci gaba da shari’a.