✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bunkasa Arewa maso Gabas: Gudunmawar Otedola ta Naira biliyan 5 ta tayar da kura

Gudunmawar da fitaccen attajirin nan dan Jihar Legas, Femi Otedola ya bayar ta Naira biliyan biyar ga Gidauniyar Sabe the Children ta Birtaniya domin taimakon…

Gudunmawar da fitaccen attajirin nan dan Jihar Legas, Femi Otedola ya bayar ta Naira biliyan biyar ga Gidauniyar Sabe the Children ta Birtaniya domin taimakon yaran yankin Arewa maso Gabas ta tayar da kura, bayan da wadansu ’yan Najeriya suka yi wa attajiran da suka fito daga Arewa gori a kai.

Wannan tallafin, wanda hatta Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo  ke ganin shi ne tallafi mafi girma da mutum daya ya yi wa yankin a tarihin Najeriya, ’yar dan kasuwan mai suna Tolani ne ta wakilci mahaifinta wajen sanar da tallafin a wani taro da ya gudana a Abuja a ranar Lahadin da ta gabata.

“Mahaifina, Mista Femi Otedola ya dade yana taimaka wa marasa karfi irin haka. Don haka ne za mu bayar da tallafin Naira biliyan 5 domin tallafa wa yaran jihohin Borno da Adamawa da Katsina ta hannun Gidauniyar Sabe the Children,” inji ta.

An shirya taron ne karkashin Gidauniyar Cuppy domin tara wa Gidauniyar Sabe the Children kudi.

Ita dai Gidauniyar Sabe the Children ita ce gidauniyar kula da kananan yara mafi karfi da girma a duniya bayan Asusun UNICEF.

Ita kuma Gidauniyar Cuppy, gidauniya ce da ’yar dan kasuwar, Florence Otedola ta assasa, kuma Jakadiya ce ta Gidauniyar Sabe the Children a Afirka.

Da take jawabi, Babbar Jami’ar Gudanarwa Gidauniyar, Kebin Watkins ta bayyana godiyarta ga Femi Otedola, sannan ta yi alkawarin cewa za a kashe kudin yadda ya kamata.

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayar da tallafin Naira miliyan 100. Dangote ya ce mutane da yawa ba sa son taimakawa, ba su san cewa, “Idan kana yawan taimakawa ba ne Allah zai kara maka,” inji shi.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osibanjo da Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole da Sanata Bukola Saraki da Ambasada Babagana Kinkige da Misis Bola Shagaya.

Daga cikin gwamnonin da suka halarta akwai Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum da na Legas Babajide Sanwo-Olu da Dapo Abiodun na Ogun.

Shi dai Otedola ya dade yana tallafa wa mutane, inda a kwanakin baya ya ba Babban Masallacin Juma’a na Kwara tallafin Naira miliyan 100 da sauransu.

Sai dai bayan bayyana tallafin, sai mutane suke ta magana kan cewa ya fi ’yan Arewa kokari wajen tallafa wa yankin.

Amma binciken Aminiya ya gano cewa, Alhaji Aliko Dangote ya bayar da tallafin da ya haura na Naira biliyan 9 ga yankin Arewa maso Gabas, duk da cewa ba a zuwa daya ya bayar ba.

A tsakanin shekarar 2012 zuwa 2018, Gidauniyar Dangote ta kashe wa ’yan gudun hijirar yankin Naira biliyan 7.

A ranar 18 Yunin bana, Dangote ya kaddamar da Kauyen Dangote, inda aka gina wa ’yan gudun hijira gidaje a kauyen Dalori da ke Karamar Hukumar Konduga. Za a gina gidaje isassu guda 200 da suka kai Naira biliyan 2 da makaranta da asibiti da filin noman rani da sauransu sannan aka ba kowane dan gudun hijira Naira dubu 100.

Sannan a watan Yunin bara, wanda ya zo daidai da watan Azumi, an raba kayan abincin da ya kai Naira miliyan 200.

Haka kuma binciken Aminiya ya gano cewa, Alhaji Mohammed Indimi ya bayar da tallafin ga yankin da ya kai Naira biliyan daya da miliyan 300.

A watan Oktoban bara, Alhaji Indimi ya gina gidaje 200 a Bama da Gamboru-Ngala, kowane kuma ya ci Naira miliyan 600. Sannan ya tallafa wa sama da ’yan gudun hijira dubu 100. Haka ya ba wa Gwamnatin Jihar Adamawa tallafin Naira miliyan 200 domin sake gina gidejen da Boko Haram suka barnata.