✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chadi: Faransa da kasashen Sahel sun amince a nada dan Idriss Deby

Faransa da kawayenta da ke yaki da kungiyar masu da’awar jihadi a yankin Sahel sun goyi bayan yunkurin nada dan shugaban Chadi da aka kashe,…

Faransa da kawayenta da ke yaki da kungiyar masu da’awar jihadi a yankin Sahel sun goyi bayan yunkurin nada dan shugaban Chadi da aka kashe, Idriss Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya.

Shugaba Emmanuel Macron da takwarorinsa na kasashen yankin Sahel sun gana da Janar Mahamat Idriss Deby kafin jana’izar mahaifinsa, inji wani jami’in fadar shugaban kasar.

Kasashen su ne Burkina Faso, Mali, Mauritania da Jamhuriyar Nijar.

Shugabannin sun nuna “hadin kan ra’ayoyi,” suna cewa “sun tsaya tare da Chadi tare da nuna goyon bayansu na bai daya ga tsarin mika mulki tsakanin farar hula da sojoji, don dorewar yankin”, inji majiyar.