✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ci-rani ya koma karkara – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yanzu mutane sun fara komawa kauyuka daga birane domin yin noma wanda a cewarsa alama ce ta ci gaban…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yanzu mutane sun fara komawa kauyuka daga birane domin yin noma wanda a cewarsa alama ce ta ci gaban kasa domin ci gaba ba ya samuwa sai an inganta rayuwa a karkara.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da yake bude wani babban kamfanin kyankyasar kaji da kiwon kaji da kuma abincin kajin da ya ci Dalar Amurka miliyan 150, (sama da Naira biliyan 54) da kamfanin Olam tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Kaduna. 

Yayin bude kamfanin Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi nasarar rage zuwa ci-rani daga kauyuka zuwa biranen inda maimakon haka yanzu ci-rani ya koma daga birane zuwa kauyukan kasar nan.

Kamfanin wanda aka gina shi a kauyen Cikibiri Gabas, Gwagwada a Kaduna, shi ne mafi girma a Nahiyar Afirka.

 Shugaban kasar wanda Ministan Gona Mista Abdu Ogbe ya karanta jawabinsa a wajen taron, ya ce yana farin cikin ganin yadda ’yan Najeriya ke murnar ganin nan ba da dadewa ba za su rabu da kuncin rayuwar da ake fama da shi wanda ya samo asali daga tabarbarewar tattalin arziki.

“Muna farin cikin ganin yadda ’yan Najeriya ke farin cikin fita daga cikin wannan kangi na tabarbarewar tattalin arziki. Kuma gwamnati ta yi nasarar rage yawan zuwa cirani daga kauyuka zuwa birane maimakon haka ci-rani ya koma ne daga birane zuwa kauyuka. Har ila yau daga cikin nasarar da muka samu a fannin noma har da irin rige-rige da kamfanoni masu zaman kansu ke yi zuwa kasar nan. A yau muna Jihar Kaduna, mako shida da suka wuce muna Jihar Kebbi. Wata hudu kuma da suka wuce muna Jihar Kano sannan nan da  makonni kadan masu zuwa za mu ziyarci wata jiha domin bude irin wannan aiki,” inji shi. 

Shugaba Buhari, “Burinmu shi ne mu ga cewa harkar gona ta samu darajar da zai taimaka wa tattalin arzikin kasar nan musamman a kokari da muke yi na rage yawan dogaro da man fetur. Wannan ya sa dole ne mu ga cewa muna iya ciyar da kanmu daga abin da muke nomawa sannan mu noma abin da za mu ci kafin mu mayar da hankali wajen magance sauran matsalolin rayuwarmu.”

Shugaba Buhari ya kara da cewa bude wannan kamfani a Kaduna ya tabbatar da maganganun da ake yi cewa tabbataccen ci gaba na samuwa ne a tattalin arziki idan ya faro daga karkara. 

A cewarsa, wata shida da suka wuce an ba da sanarwar Najeriya na fama da masassarar tattalin arziki kuma tunda daga lokacin gwamnati ta tashi tsaye wajen ganin ta magance matsalar. Ya ce duk da wannan nasara akwai bukatar gwamnati ta kara kaimi wajen magance matsalar tattalin arziki da kasar ke fama da shi.     

A jawabin Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya ce kamfanin Olam zai rika kyankyasar ’ya’yan tsaki sama da miliyan daya da dubu 600  a kowane mako idan ya fara aiki sosai. Ya ce  gwamnatinsa ta gayyaci kamfanin ne zuwa Kaduna a kokarinta na rage dogaro da kudin man fetur.

“Wannan kamfani zai taimaka matuka wajen samar da ayyukan yi ga matasa da sauran jama’ar jihar sannan kananan manoma za su yi matukar amfana da ayyukan kamfanin,” inji shi.