✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ciwon barci

Ina so a yi mana bayani ne a kan ciwon barci wato sleeping sickness, domin na ji kamar wai akan iya daukarsa daga uwa zuwa…

Ina so a yi mana bayani ne a kan ciwon barci wato sleeping sickness, domin na ji kamar wai akan iya daukarsa daga uwa zuwa jariri. Wato shin ana iya gadar ciwon ke nan?
Amsa: Akwai abubuwa da dama da kan kawo ciwon barci, wanda alamunsa shi ne yawan barci. Na farko shi ne shigar kwayoyin cuta na trypanosoma masu sa ciwon barci, sakamakon cizon kudan tsando. Shi wannan kuda daga jikin shanu yake zuko kwayar cutar ya sa wa mutum ta hanyar cizo. Wato ke nan an fi samun matsalar a masu kiwon shanu ko masu harka da shanu. An fi samun ciwon a tsakanin Fulanin kasashen Kwango da Kamaru fiye da na Najeriya.
Kafin yawan barci, sai mutum ya fara jin alamu kamar na zazzabin maleriya wato ciwon kai, ciwon jiki, kasala da ciwon gabobi. Su ma shanu masu dauke da wannan kwayar cuta suna yawan samun barcin. Idan mutum na harka da shanu kuma yana samun irin wadannan alamu da kuma yawan barci, to ya je asibiti a bincika ko matsalar ce, domin akwai magani. Idan kudan ya ciji wata mata mai juna-biyu, kwayar cutar za ta iya bi ta mahaifa ta shiga jinin abin da ke ciki, shi ma ya kamu da cutar ke nan.
Bayan wannan akwai ciwon kiba da minshari. Mai ciwon kiba wanda kuma su suka fi yin minshari, kullum a cikin barci suke, musamman ma barcin rana, domin ba su cika samu da dare ba sosai. Maganin irin wannan yawan barci shi ne rage kiba.
Akwai kuma ciwon damuwa, wanda kan iya sa yawan barci. Shi wannan a kwakwalwa matsalar take kuma shi ne ake ganin za a iya gado daga uwa zuwa danta, amma yawanci sai an girma ake gani, ba a kuruciya ba.
A karshe, sai yawan shaye-shayen magungunan maye barkatai masu bugarwa, kamar baliyam ko sholisho ko ruwan barasa da dai sauransu.
Sauran tambayoyi
Wai me ke haddasa cutar ciwon suga, kuma da gaske ne idan mai ciwon suga ya ji rauni ba ya warkewa?
Daga Abubakar Lawal, Daura.
Amsa: Ciwon suga iri uku ne: Akwai wanda akan gada a wurin iyaye ko kakanni, wanda ko kananan yara za su iya samu; akwai kuma wanda kiba kan jawo; sai kuma wanda wasu mata masu juna biyu kan samu. Yawanci wannan na ukun da mace ta haife yake tafiya, amma takan iya shiga hadarin kamuwa da iri na biyun a wasu lokuta, idan ta kara manyanta, musamman ma idan tana da kiba.
Ta bangaren rauni, gaskiya ne mai ciwon suga, wanda ba ya shan maganin ciwon, wato wanda suga ya fara yawa a jininsa, idan ya yi rauni ciwon zai dade kafin ya warke. Sugan yana rage karfin garkuwar jiki, kwayoyin cuta kuma su cika wurin saboda su ma suna bukatar sugan, kuma shi sugan yana shiga raunin ta hanyoyin jini ya hana wurin warkewa. Ke nan dole sai an sha magunguna, suga ya yi kasa kafin ya warke.
Da gaske ne mai shan taba sigari idan ya ji rauni wurin yakan dade kafin ya warke?
Daga Abdullahi, Gabasawa
Amsa: Haka ne, ita ma taba sigari, kamar yawan suga, gubarta takan iya sa garkuwar jiki ta yi kasa, jikin mutum ya kasa yakar cuta ko ya kasa samar da sinadaran da ake bukata wajen warkar da raunin. Sa’annan masu shan sigari ba su da karkon fata; dan shekaru arba’in mai shanta fatarsa kamar ta dan shekara hamsin take, haka ma dan shekaru sittin mai shanta fatarsa kamar ta dan shekaru saba’in take.
Wai rashin sinadaran bitamin na rukunin C zai iya kawo ciwon sanyi?
Daga Aminu, Minna
Amsa: A’a, ciwon sanyi shi dauka ake daga wani zuwa wani, wato daga mace zuwa namiji ko daga namiji zuwa mace. Rashin sinadarin bitamin C sai dai ya hana rauni warkewa ko kuma ya sa rashin kwarin fata kamar ta lebba, kullum a bushe, kullum a fashe.
A makonnin da suka wuce ka yi magana a kan toshewar magudanan jini, amma ba ka yi maganar alamomin da mutum zai ji ya gane yana tare da wannan matsala ba. Kuma ya za a sha man zaitun din?
Daga Aminu Garba, Kano da Maman Mus’ab, Zariya
Amsa: Ai yawanci a wannan matsala, duk abin da aka ji na alamu, to zance ya baci, domin abu ya riga ya yi nisa ke nan. Wato ba wasu alamu sai magudanar jinin ta toshe gaba daya ake ganewa. Wannan shi zai samar da alamun da ake ji na kullewar tsakiyar kirji a yayin bugun zuciya, da kuma yankewar jiki a fadi idan a kwakwalwa ne, hade da shanyewar bari daya na jiki. Shi ya sa a taken rubutun aka ce ‘Kariya’ saboda shi ne rigakafi kuma shi ne maganin, domin idan har an samu toshewar karamar magudanar jini gaba daya da wuya wannan magudanar jinin ta dawo aiki yadda ya kamata.
Yadda ake girki da sauran mayukan girka abinci haka ake amfani da man, wato ana so idan da hali a rika girki da man zaitun wato olibe oil ko da jefi-jefi ne.
Wai da gaske ne cin kabeji yana iya kawo makoko?
Daga Maman Faruk
Amsa: E, shi kabeji yakan iya rage yadda jikinmu ke tsotse sinadarin iodine a abinci, wanda rashinsa kan iya kawo makoko. A mutanen da ba sa samun gishiri ko ruwa mai dauke da sinadarin iodine, za a iya samun haka. Amma da yake a yanzu kusan kowane irin gishirin dafa abinci ana sa masa wannan sinadari na iodine, kuma akan samu a ruwan shanmu, zai wahala a ce cin kabeji kawai ya kawo ciwon makoko, sai dai wani abu daban. Saboda wadannan matakai guda biyu da aka dauka a duniya, wato na kara sinadarin iodine a ruwan sha a matatun ruwa, da kara wa gishiri a kamfanonin yin gishiri, an rage samun makoko sosai a yanzu.
Kwanan baya ka ba wani amsa cewa ya daina kara gishiri danye a abinci sai dai a dafa da abincin. To su irin su danwake da wake da shinkafa da ake sa musu barkono mai gishirin da ba a dafa ba fa?
Daga Injiniya dahiru kofar Marusa da Alhaji Zubairu Garabasa
Amsa: E, to sai dai mu ce a sa gishirin dan diris a barkonon, wato a dai ci a hankali. Da yake shi Malam Bahaushe ya riga ya saba wa harshensa da dandanon gishiri, shi ya sa yake daya daga cikin al’ummar da suke kan gaba wajen samun hawan jini.