✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Cutar maleriya na barazana a Afirka’

Sabon rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa  cutar maleriya tana kashe sama da mutum dubu hudu a kowace shekara saboda rashin tallafin…

Sabon rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa  cutar maleriya tana kashe sama da mutum dubu hudu a kowace shekara saboda rashin tallafin yaki da cutar. Hukumar WHO ta ce rabin al’ummar duniya na cikin hadarin kamuwa da cutar.

Miliyoyin mutane na kamuwa da cutar musamman kananan yara da mata masu juna biyu a kasashen Afirka. Rahoton ya nuna takaicin yadda cutar maleriyar ke ci gaba da zama barazana sakamakon jan kafa na samun kudaden yaki da cutar baki daya.

Sabon rahoton na WHO ya ce an samu raguwar hadarin kamuwa da cutar a bara idan aka kwatanta da shekarar 2017, amma duk da haka hukumar ta yi  kira ga kasashen da cutar ta fi kamari su dage wajen magance ta.