✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dagaci da dansanda sun rasa rayukansu a rikicin kabilun Benuwe da Nasarawa

’Yan bindiga jiya sun kashe Cif Iyongovihi Ninge, dagacin garin Chembe da ke kauyukan Ukemberagya da Tswarev da ke mazabar Gaambe-Tiev da ke yankin karamar…

’Yan bindiga jiya sun kashe Cif Iyongovihi Ninge, dagacin garin Chembe da ke kauyukan Ukemberagya da Tswarev da ke mazabar Gaambe-Tiev da ke yankin karamar hukumar Logo na jihar Benuwe.
 
’Yan sanda sun tabbatar da mutuwar dan sandan kwantar da tarzoma daya a sabon rikicin da ya barke tsakanin fulani makiyaya da ’yan kabilar Tibi a kauyen Obi da ke karamar hukumar Keana da ke jihar Nasarawa.
 
Wadanda lamarin ya auku a kan idonsu sun ce dagacin wanda ke Benuwe ya je gonarsa don ya duba yadda ma’aikata ke aiki ke tuna inda zai shuka doya sai kwatsam makiyaya suka bullo suka harbe shi nan take.
 
Shaidun sun tabbatar da cewa  sun tabbatar da cewa mai sarautar ya mutu nan take sannan kuma wadanda ke aiki a gonar suka gudu yayin da fulanin suka mamaye gonar.
Shugaban karamar hukumar Logo, Richard Nyajo ya ce ya samu rahoton cewa wasu da a ke zargi fulani makiyaya ne sun kashe dagacin Chembe inda suka tarwatsa mutanen kauyen da harbin kan-mai-uwa da –wabi.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Benuwe, Fatai Owoseni ya ce har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai samu rahoton lamarin ba.