✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dagatai da masu unguwanni na da hannu a rikicin Fulani da Makiyaya a Jigawa’

Ba za a iya magance matsalar rikicin manoma da makiyaya da yake neman ta’azzara ba sai dai idan Fadar Mai martaba Sarkin Hadeja ya sanya…

Ba za a iya magance matsalar rikicin manoma da makiyaya da yake neman ta’azzara ba sai dai idan Fadar Mai martaba Sarkin Hadeja ya sanya hannu wajen kiran taron zaman sulhu saboda dagatai da masu unguwanni suna da hannu wajen rura wutar rikicin manoma da makiyaya a yankin masarautar.

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Kungiyar Dattawan Fulani makiyaya mai kula da shiyyar Jigawa da Jamhuriyyar Nijar Malam Isah Lutti a wajan taron sulhu tsakanin manoma da makiyaya da Gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya a Karamar Hukumar Guri

Taron ya biyo bayan wani mummunan rikici da ya barke a Karamar Hukumar Guri tsakanin manoma da makiyaya har aka samu asarar rayuka na mutum hudu kuma amfanin gona mai yawa ya salwanta a rikicin, wanda ya sa Fulanin suka fatattaki manoma daga kauyukansu suka koma Hadejiya suna gudun hijira.

Malam Isah Lutti ya bukaci Fadar Mai martaba Sarkin Hadejiya ta zauna da shugabannin kungiyar manoma da na Fulani domin a gano inda matsalar take a magance ta, sannan ya ce muddin ba a zauna an yi maganin rikicin ba, ba za a samu fahimtar juna ba.

Ya kara da cewa sun yi iyakacin bincike a kan matsalar rikicin, amma sun gano cewa babu hannun Fulanin yankin a cikin wannan rikici da aka yi, sannan ya ce idan gwamnati ta yi sakaci har wasu bakin Fulani suka shigo cikin rikicin, to shawo kan matsalar zai yi wahala.

Lutti ya ce babu masu rura wutar rikicin tsakanin manoma da Fulani kaman shugabannin kananan hukumomi da dagatai da masu unguwanni saboda suna da wata bukata ta kashin kansu.

Don haka ya bukaci maimartaba sarkin Hadejiya ya kira taron gaggawa tsakanin bangarorin biyu don ganin an kawo karshen matsalar.