✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dakataccen Shugaban PDP Na Jihar Ondo Ya Rasu

Dakataccen Shugaban PDP a Jihar Ondo, Fatai Adams ya rasu, kwanaki 43 bayan dakatar da shi daga am’iyyar.

Dakataccen Shugaban PDP a Jihar Ondo, Fatai Adams ya rasu, kwanaki 43 bayan dakatar da shi daga jam’iyyar.

Fatai Adams, ya rasune sakamakon ciwon kai a gidansa da ke Ikare Akoko a daren Talata.

Kwamitin Gudanarwan PDP na jihar sun dakatar da Adams ne a ranar 2 ga Janairu, 2024 saboda zargin zagon gaka ga jam’iyyar.

An kuma zarge shi da yin wasu abubuwa da ka iya janyo wa jam’iyyar adawar abin kunya.

Dakatarwar ce ta ba da damar zaman Mista Tola Alabere shugaban riko.

Mun kasa samun kakakin jam’iyyar PDP na jihar, Kennedy Peretie domin jin ta bakinsa kan lamarin.