✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daki ya zube a kan wata tsohuwa a Kaduna

A ranar Larabar makon jiya ce wani abin tsautsayi ya faru a Layin Fulani Road da ke Tudun Wada Kaduna lokaci da dakin wata tsohuwa…

 Dakin da ya rushe a kan tsohuwa Sa’adatu. A ranar Larabar makon jiya ce wani abin tsautsayi ya faru a Layin Fulani Road da ke Tudun Wada Kaduna lokaci da dakin wata tsohuwa mai suna Sa’adatu ya rushe a kanta inda da kyar da jibin goshi matasan unguwa suka ceto ta aka garzaya da ita asibiti rai kwakwai mutu kwakwai.
Tsohuwar mai kimanin shekara 80 tana kwance a dakinta tana barci ne saboda rashin lafiyar da take fama da shi. dakin  ya rushe sakamakon ruwan saman da aka sheka kamar da bakin kwarya a daren Talata zuwa wayewar garin Larabar da al’amarin ya faru.
’Yar uwar Sa’adatu mai suna Maimuna da abin ya faru a kan idonta ta bayyana wa wakilinmu cewa, a lokacin da take wanke kaya a kusa da dakin tsohuwar a harabar gidan da misalin karfe goma sha daya na safe, sai ta lura dakin ya fara motsi yana neman zubewa. Ta ce nan da nan ta sanar da Sa’adatu halin da ake ciki amma duk da kwala mata ihu ba ta ji ba har sai da ginin ya zube.
Maimuna ta ce daga nan ne Sa’adatu ta rika ihu tana neman agaji, ita kuma ta fita waje don neman agaji inda ta sanar da matasa halin da ake ciki.
Ta ce, matasan ne suka shiga gidan suka zakulota aka garzaya da ita asibiti don yi mata magani.
Maimuna ta ce babu wanda ya zaci za a zaro tsohuwar da rai.  “Mun gode Allah da abin ya tsaya a kan raunukan da ta samu, domin a lokacin da aka zaro ta, mun dauka ba ta da rai,” inji ta.
Ta ce, bayan an dawo da ita daga asibiti an canja mata wani daki a gidan Mai unguwar Tudun Wada, Malam Isiyaku Hassan Madaki don ci gaba da yin jinya a can.
A lokacin da wakilinmu ya ziyarci tsohuwa Sa’adatu a gidan Mai unguwa Isiyaku ya tarar da ita a cikin daki tana kwance tana jinyar raunukan da ta samu.
Tsohuwa Sa'adatuTa yi godiya ga Allah da Ya kubutar da ita daga wannan tashin hankali da ta tsinci kanta a ciki.
Daga nan ta yi kira ga hukuma ta kawo mata daukin gaggawa ganin dakin da ta mallaka ya rushe, kuma ba ta da kudin da za ta sake gina wani. Sannan ta gode wa mai unguwar bisa taimakon da ya yi mata na ba ta dakin da za ta ci gaba da zama har ta murmure.
Rushewar gine-gine a yankin Tudun Wada da kewaye ta faru a ranar Larabar sakamakon ruwa kamar da bakin kwarya inda gine-gine da dama suka fadi musamman gine-ginen kasa.