Dubun wasu daliban jami’ar Adekunle Ajasi (AAUA) da ke jihar Ondo wadanda ake zargi da kashe Abokin karatun su ta cika bayan da tawagar rundunar ‘yan sandan jihar mai yaki da ‘yan kungiyar asiri suka yi masu kofar rago.
A cewar kwamishinan ‘yan sandan jihar Ondo Undie Adie, daliban da ake zargi wadanda suka shiga komar ‘yan sandan sun hadar da Ifedayo Oluwaseun mai shekaru 19 da Nafiu Akani David mai shekaru 22 Ajibola Philips mai shakaru 22 ya ce, wadanda ake zargin sun amsa laifin su, su ka ce su ‘yan kungiyar asiri ta Aiye ce kuma sun kashe abokin karatun su mai suna Daniel Paul mai shakaru 21 a wani kungurmin jeji a lokacin da suke rantsar da sabbin manbobin kungiyar, ” Dalibin da aka kashe yana karantar fannin falsafa ne shekarar sa ta biyu a jami’ar, waxanda ake zargin na ci gaba da bada muhinmman jawabai kana rundunar mu na kokarin kamo ragowar ‘yan kungiyar da su ka gudu
tuni dai hukumar jami’ar ta kafa kwamiti domin bincikar lamarin.