✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dambarwa 5 a kwana 10 na sabon Gwamnan Filato

Tun ranar da aka rantsar da Gwamna Caleb ya fara yamutsa hazo a Jihar Filato

Filato na daga cikin jihohin da aka sami canjin jam’iyya mai mulki a zaben kujerar Gwamnan da ya gabata.

An sami canjin ne daga Simon Lalong na Jam’iyyar APC da ya yi shekaru 8, zuwa Barista Caleb Mutfwang na Jam’iyyar PDP, wanda ya lashe zaben.

Daga ranar da aka rantsar da Barista Caleb ya yi wasu nade-nade uku da suka yamutsa hazo a jihar.

Gadon bashin biliyan 200

A jawabinsa na karbar mulki ne Gwamna Caleb Mutfwang, ya ce ya gaji bashin Naira biliyan 200 daga tsohuwar gwamnatin jihar, ga shi kuma bangaren kiwon lafiya na bukatar kulawar gaggawa.

A cewarsa, duk da cewa zai i kokarin samar da ci gaba, amma “babu hanyoyin magance wadannan kalubale cikin gaggawa, amma a shirye muke mu dauki kalubalen gaba-gaba don warware su.”

Nadin ba-zata

Nadin da ya yi wa Samuel Nanchang Jatau a matsayin sakataren gwamnatin da Barista Philemon Dafi matsayin Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar, da kuma Moses Nwan a matsayin Sakataren Gwamnan na musamman, ya jawo ce-ce-ku-ce.

Da farko ana zargin wasu ne za su rika juya akalar Gwamna Caleb, amma sanya’yan hannun damansa a kan wadanna mukamai da ya yi, ya sa kallo ya koma sama.

Dambarwar dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi

Wata kura da Gwamna Caleb ya tayar bayan rantsar da shi ita ce ta amincewarsa da dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar 17, wadanda Majalisar Dokokin Jihar ta yi, bisa zargin almundahanar kudaden Kananan Hukumominsu.

Amma a wani taron ’yan jarida da suka kira a Jos, shugabannin kananan hukumomin sun bayyana cewa gwamnan da majalisar ba su da hurumin dakatar da su.

Haka kuma sabon gwamnan, ya rushe dukkan wasu masu rike da mukamain siyasa, a dukkan hukumomin jihar.

Masaukin alhazai

Hawan Gwamna Caleb ke da wuya ya ci karo matsalar masaukan alhazan jihar a Kasa Mai Tsarki, inda suke fama da karancin jami’an kula da lafiyarsu da kuma malamai masu wa’azi, saboda tsohuwar gwamnatin ba ta biya wasu kudade ba.

Duk da cewa matsalar ta tayar da kura sosai, amma sabon gwamnan ya ba da tabbacin cewa jami’an da ba su samu tafiya ba za su tafi, kuma za a samar wa alhazan masaukai masu kyau kuma za a tura musu karin jami’an lafiya.

A jawabin gwamnan na karbar rantsuwa ne ya ayyana dokar ta-baci kan tsaftace muhalli a jihar, kuma nan take ya kafa kwamitin tsaftar muhalli da ya fara aikin kwashe duk wata shara da ke garin Jos da kewaye. Ya zuwa yanzu an kwashe shara mai tarin yawa a cikin garin Jos da kewaye.