✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Adam Zango ya zama mawakin Hip-Hop

Haidar Adam, dan fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya kammala daukar bidiyon sabon kundin wakokinsa mai suna ‘Take Over’.   Aminiya…


Haidar Adam, dan fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya kammala daukar bidiyon sabon kundin wakokinsa mai suna ‘Take Over’.
 
Aminiya ta samu tabbacin cewa an dauki albam din a Kano ne, kuma yana kunshe da wakoki uku da suka hada da ‘Godiya’ da ‘Rayuwa’ da kuma ‘Taken Over’
 
Aminiya ta tabbatar da cewa a kwanakin baya Haidar wanda a yanzu ake yi masa lakabin Star Boy ya cika shekara 11.
 
Star Boy wanda a shekarun baya ya fito a cikin fitaccen fim din ‘Ummi’ an nuno shi a tallar bidiyon albam din yana waka cikin harshen Hausa da kuma Turanci.
 
Kamfanin White House Family da na MSK Records suka dauki nauyin shirya albam din, inda MSK ya bada umarni.