✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Indiya mai bauta wa Shugaba Trump ya fadi dalilinsa

Duk da yadda Amurkawa ke nuna matukar goyon baya ga Shugaba Donald Trump, ba su kai wani dan kasar Indiya ba. Mutumin mai suna Bussa…

Duk da yadda Amurkawa ke nuna matukar goyon baya ga Shugaba Donald Trump, ba su kai wani dan kasar Indiya ba. Mutumin mai suna Bussa Krishna ya koma yana bauta wa Shugaba Donald Trump a matsayin ubangijinsa.

Kafar labarai ta odditycentral.com ta ce, Bussa Krishna, yana bauta wa mutum-mutumin Trump da hotonsa ne ta hanyar kada kararrawa da kuma ajiye furanni a wani bango da ya gina da kansa.

Bussa, mai shekara 33 dan asalin kauyen Konne da ke Jihar Telengana ta kasar Indiya ya jawo hankalin kafafen watsa labarai ne ’yan shekarun da suka gabata lokacin da hotunansa suka yadu a shafukan Intanet, wadanda aka dauke shi yana bauta wa mutum-mutumin Trump a wani bigire da ya gina.

Shugaba Trump ya kai ziyarar kwana biyu a kasar Indiya inda batun mutumin ya sake jawo hankalin kafafen watsa labarai. Kuma duk da abubuwan da suka faru ’yan shekarun nan bai girgiza Mista Bussa ba a kan bautar da yake yi wa Trump ba.

Mista Bussa, ya fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na ANI cewa, “Ina son dangantakar Amurka da Indiya ta sake karfafa. A kowace ranar Juma’a nakan yi addu’a ga Trump ya samu nisan kwana. Ina kuma daukar hotonsa in yi masa bauta kafin in tafi wurin aikina. Ina matukar son in hadu da shi kuma ina rokon gwanmati ta taimaka min in samu haduwa da shi.”

An ruwaito cewa, Bussa wanda yanzu aka kira da “Trump-Krishna” ya shiga bauta wa Trump ne saboda inganta huldar jakadanci da ke tsakanin kasashen biyu. Hakan ne ya sa ya fara bauta wa Trump tun shekara uku da suka wuce bayan kisan gillar da aka yi wa wani injiniya dan asalin Jihar Telengana a kan laifin nuna kiyayya. Yana fata cewa, abin da yake yi zai gamsar da Shugaban a madadin sauran ’yan kasar ta Indiya.

A bayanin da ya yi a wata hira da aka yi da shi a shekarar 2018 ya ce, “Kisan ya dame ni sosai. A tunanina, ta wannan hanyar ce kawai Shugaban Amurka da sauran Amurkawa za su fahimci matsayin kasar Indiya ta hanyar nuna so da kauna. Wannan ne ya sa na fara bauta masa tare da fatar wata rana za mu hadu da shi.”

“Na yi amanna cewa, mutanen Indiya za su iya samun nasara a kan kowa, amma a yayin da mutum ya kasa samun taimako daga wani babba, to ana iya nasara ta hanyar nuna so da kauna kuma shi ne abin da nake yi,” inji shi.

Duk da cewa, ya yi ikirarin gina babban wurin bauta amma shekara biyu ke nan yana ci gaba da bautar a gaban hoton Shugaba Trump, mai girman kafa shida a gonarsa da   ke garin Konne.

“Nakan dauki hotonsa tare da ni kuma nakan bauta masa kafin in yi kowane irin aiki. Yana nan kamar ubangiji ne a wurina kuma hakan ne ya sa na gina mutum-mutuminsa wanda ma’aikata 15 suka gina shi a wata daya,” inji shi

Mazauna kauyen da dama ’yan uwan Mista Bussa Krishna, sun ce sun dauka hauka ce ta same shi, amma yanzu sun fahimci cewa, tsananin soyayya ce yake yi wa Shugaba Trump. Sun taya shi kira ga gwamnati ta cika masa burinsa na haduwa da Shugaban musamman lokacin da yake ziyara a kasar.