✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan jarida

Wani dan jarida ne yana cikin tafiya a mota sai ya ga mutane sun taru a gefen titi, alamar an yi hatsari. Nan da nan…

Wani dan jarida ne yana cikin tafiya a mota sai ya ga mutane sun taru a gefen titi, alamar an yi hatsari. Nan da nan ya ratse gefen titi, ya dauki kayan aikinsa ya nufi wurin. Da ya ga ya kasa shiga don ya yi hira da wanda aka buge din sai ya kama fada wa mutane cewa: “Don Allah ku kauce, wanda motar ta buge, ni danta ne.” Sai mutane suka matsa ya shiga zuwa wurin. Yana shiga sai ya ga ashe akuya ce mota ta kashe.
Daga Kabir SKB Rikkos-Jos, 08182534573