✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan shekara 14 ya kashe budurwa wurin sayen burodi

Wani yaro dan shekara 14 mai suna Isma’ila Idris ya caka wa wata budurwa almakashi a wuya ta mutu lokacin da suke takaddama kan sayen…

Wani yaro dan shekara 14 mai suna Isma’ila Idris ya caka wa wata budurwa almakashi a wuya ta mutu lokacin da suke takaddama kan sayen burodi a garin Bauchi.Yaron wanda yanzu haka ke hannun ’yan sanda kamar yadda kakakin ’yan sandan Jihar Bauchi Haruna Mohammed ya tabbatar wa manema labarai dan Unguwar kofar Gombe ne da ke cikin garin Bauchi kuma ya caka wa abokiyar takaddamarsa mai suna Ramatu Aminu mai shekara 18 almakashi ne a wuya a wani gidan burodi da ake kira Haske da ke bayan makarantar Firamare ta Shekel a Unguwar Shekal da ke garin Bauchi a ranar Alhamis din makon jiya.

Isma’ila wanda ake wa lakabi da Shaidan ya kashe Ramatu lokacin da ta je gidan burodin domin sari kamar yadda ta saba.
Mahaifin marigayiyar Malam Aminu Mahmud ya shaida wa wakilinmu cewa Ramatu ta je gidan burodin Haske ta zabi wasu burodi manya ta ajiye a gefe, sai Sama’ila Shaidan ya zo ya dauki burodin da ta zaba.
Ya ce da ta ce masa yaya zai dauka mata burodin da ta zaba ne, sai cacar baki ta kaure a tsakaninsu inda ya fito da almakashi daga cikin aljihunsa sai ya soka mata a wuya nan take ta fadi kafin a je asibiti Allah Ya yi mata rasuwa.
Ya ce wadanda abin ya faru kan idonsu sun ji lokacin da suke cacar baki yana cewa zai huda ta da almakashi, kuma sai ga shi ya aikata abin da ya fada.
Malam Aminu ya ce an kawo wa Ramatu sadaki da kayan aure saura kwanaki kadan ya rage a daura mata aure sai Shaidan ya halaka ta. “Mun yi niyar za mu daura mata aure sai wanda ya kawo mata sadaki ya ce a ba shi lokaci domin ya samu damar kammala wasu gyare-gyare,” inji shi.
Majiyar Aminiya ta ce Sama’ila Shaidan yana zaune ne a unguwar, yayin da mahaifinsa yake zaune a Unguwar Jahun. Kuma a cewar majiyar idan yana husuma da yara ko aka yi masa wani abu sai ya ce “sai na kashe ka, wannan shi ne kalmar da ke yawan fita daga bakinsa,” inji majiyar.
Kuma mahaifin marigayiyar ya ce bayan abin ya faru iyayensa sun je sun yi musu ta’aziyyar abin da ya faru. Haka mai gidan burodin da mahaifinsa sun je sun yi musu ta’aziyya.
Ya ce, “Za mu dauki mataki daidai bakin gwargwado amma yanzu muna jira mu ga matakin da ’yan sanda za su dauka a kan Sama’ila. Hakika ba za mu yafe ba, saboda akwai matasa da dama a wannan unguwa da suka sha kashe ’ya’yan mutane ana zuba musu ido. Ya kamata kowa ya shafa wa kansa lafiya domin daga yanzu za mu rika daukar mataki a kan duk wanda ya yi sanadiyar kashe wani ko wata.”