✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan siyasa ya koka da yanayin zaben kananan hukumomi

Wani dan siyasa da ke zaune a Kalaba Jihar Kurosriba, Alhaji Bara’u Musa ya bayyana rashin gamsuwa da yadda Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da…

Wani dan siyasa da ke zaune a Kalaba Jihar Kurosriba, Alhaji Bara’u Musa ya bayyana rashin gamsuwa da yadda Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da zaben kananan hukumominta a kwanakin baya, inda ya ce yanayin zaben tamkar zubar da mutuncin jiha da na Jam’iyyar APC ne.

Ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakilinmu. “Kowa yana ganin jam’iyyar APC a matsayin jam’iyyar canji, ana sa ran ta kawo canji sai ga shi maimakon ta fitar da jaki daga dan duma tana neman kasawa. An yi duk irin badakala da tabargaza a zaben Kano amma Gwamnatin Tarayya da Hukumar Zabe ta kasa duk babu wani wanda yayi magana.

“Idan gwamnati da hukumar zabe ba su yi magana ba, to nan gaba fa kowa na iya yin abin da ya ga dama a jiharsa idan ya tashi yin zabe. Domin an nuna abin mamaki irin yadda ta kafafen sada zumunta aka baza hotunan yara kanana suna dangwalen kuri’a har suna nuna yatsunsu amma babu wani wanda ya yi Magana. Shi ya sa ni nake ganin zubar da mutuncin jam’iyya ne, haka nan kuma shi zai hana dan takara fitowa zabe ko mai jefa kuri’a domin ana yi wa jama’a karfa-karfa,” inji shi.

Ya nuna shakkun cewa matukar an bari kowane gwamna yana yin abin da ya ga dama a jiharsa idan zabe ya zo, to sannu a hankali masu zabe za su dawo daga rakiyar fita rumfunan zabe domin maganar yin amfani da al’umma a yi zabe ta kaura ke nan; jam’iyya ta dauko abin da jam’iyyar adawa PDP ta rika yi a nata lokacin. Daga nan ya nuna takaicins na kin yin magana ko tsawatarwa da jam’iyya matakin kasa ta yi.